Wallahi Ko a 2019, Abba Gida Gida Ya Ci Zaben Gwamnan Kano - 'Yar APC Ta Fasa Kwai

Wallahi Ko a 2019, Abba Gida Gida Ya Ci Zaben Gwamnan Kano - 'Yar APC Ta Fasa Kwai

  • Hajiya No Shaking ta ce a zaben Gwamnan jihar Kano da aka yi a 2019, Jam’iyyar PDP ce tayi nasara
  • ‘Yar siyasar tayi ikirarin Abba Kabir Yusuf ya doke Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a hakikanin zabe
  • Jagorar ta APC ba ta ganin Nasiru Gawuna a kusa da karagar mulki, ta jinjinawa Rabiu Kwankwaso

Kano - Wata mata da aka bayyana da Hajiya No Shaking, ta fito ta ce jam’iyyar APC ta sha kashin da ba za ta iya tashi ba a hannun NNPP a jihar Kano.

Duk da ita ma ‘yar jam’iyyar APC ce, Hajiya No Shaking ta fadawa gidan rediyon Nasara FM cewa ko a 2019, Abba Kabir Yusuf ne ya yi nasara.

‘Yar siyasar ta nuna magudi aka yi har Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zarce a kan mulki bayan wankin hula ya kai dare a zaben Gwmanan 2019.

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: Tsohon Gwamnan Arewa Mai Yakar APC Ya Yi Kus-Kus da Kwankwaso

Ganduje
Ganduje da Tinubu Hoto: www.citypeopleonline.com
Asali: UGC

Wannan karo tun da jam’iyyar NNPP ta samu nasara karara, Hajiya No Shaking ta ce babu wani dalilin da ‘ya 'yan APC za su rika yi wa kansu karya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A hirar da aka yi da ita, No Shaking ta ba ‘ya ‘yan jam’iyyarsu shawara su taya Abba K. Yusuf da addu’a domin ta tabbata shi ne zai karbi gwamnati.

No Shaking ta ce ba za ta yiwu a rubuta littafin siyasar kasar nan ba tare da Rabiu Musa Kwankwaso ba, ta ce tsohon Gwamnan gwarzo ne a yau.

Maganar No Shaking a rediyo

"Don Allah ka saurari magana ta, maganar gaskiya ayi ta da wando, bai kamata mu rika yin karya ba.
Tsaya ka ji, Wallahi a baya Abba ne ya ci zabe (2019), ya muka yi? A lokacin bayan da aka yi ‘inconclusive’ dinnan, tun da Ganduje aka ba, mu ka hakura mu ka bi.

Kara karanta wannan

"Atiku Shi Kadai Ya Aikata Abinda Kowa Ya Kasa Yi Tun 1999": Fani-Kayode Ya Zolayi Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

To yanzu aka yi juyi, ka san mulki da iko mallakar Allah (SWT) ne, Ya na badawa ga wanda Ya so a lokacin da Ya So.
Mu rungumi kaddara, mu taya Abba addu’a, shi ne ya kamata mu yi. Kuma ni dinnnan, na sha shiga rediyo in ce a gyara, a taimaki ‘yan jam’iyya.
Na ce a taimake su, aka ki taimakonsu. A yau aka yi mana war-was mu ka fadi zabe. Menene na mu za mu rika yin ihu a kai? Bai kamata ba. Ana karya…kotu, kaza-kaza...

Kwankwaso ya hadu da Bola Tinubu

Ana jita-jita cewa zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi kus-kus da Rabiu Kwankwaso a Turai, mun kawo rahoton zancen da Bashir Ahmaad ya yi.

Mun kuma ji ra’ayin wani matashin Bakwankwashe game da yiwuwar Tinubu ya jawo tsohon Gwamnan Kano, ya ba shi mukami a gwamnatinsa ta APC.

Kara karanta wannan

Abubuwa 2 Rak Za Su Hana Abba Kabir Yusuf Zama Gwamnan jihar Kano – Jagoran APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng