Jerin Gwamnoni Masu Barin Gado Da Za Su Bar Magadansu Da Biyan Bashin Albashin Ma'aikata
A yayin da ake tunkarar miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, aƙalla zaɓaɓɓun gwamnoni bakwai za su kwana da shirin fuskantar fushin ma'aikata a jihohinsu.
Dalilin hakan kuwa shine gwamonin da za su gada za su bar su da bashin biyan ma'aikata haƙƙoƙin su, da zarar sun karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Wani rahoton jaridar Punch ya yi duba kan gwamnoni masu barin gado da ake bi bashin albashi, da magadansu waɗanda za su gaji ƙalubalen biyan kuɗin.
1. Okezie Ikpeazu, jihar Abia
A jihar Abia, gwamna Okezie Ikpeazu, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akwai bashin albashin wata 30 na ma'aikanta a kansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cikin ƴan kwanakin nan ƙungiyar ƙwadago (NLC) ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani kan rashin biyan albashi.
Dr Alex Otti, wanda ya zama zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), dole ne ya nemo hanyoyin biyan wannan bashin albashin idan ya hau mulki.
2. Samuel Ortom, jihar Benue
Gwamna Samuel Ortom, shi ma na jam'iyyar PDP, ma'aikata na bin shi bashin albashi a jihar Benue.
Ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NMA) ta zargi gwamnan da ba ma'aikatan lafiya ciwon kai, kan rashin biyan su bashin albashin su.
Malaman makaranta a matakin ƙananan hukumomi na bin gwamnan bashin albashin wata 11, yayin da sauran ma'aikata a matakin ƙananan hukumomi suka biyo bashin albashin wata 10.
A matakin jiha kuwa, ma'aikata sun biyo bashin albashin wata takwas, sai yan fansho na bin bashin albashin wata 38, a cewar ƙungiyar ƙwadago.
Nan da ƴan kwanakin kaɗan zai ɗorawa Rev Fr Hyacinth Alia na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), wanda zai gaje shi, nauyin biyan wannan bashin.
3. Simon Lalong, APC
Jihar Plateau a ƙarƙashin gwamna Simon Lalong na APC, yanzu haka komai ya tsaya saboda yajin aikin sai ta baba ta gani da ƙungiyoyin ƙwadago suka shiga, a cewar The Punch.
Nauyin biyan bashin albashin zai rataya ne akan gwamna mai jiran gado, Caleb Muftwang na jam'iyyar PDP.
4. Darius Ishaku, PDP
Kusan kowane irin ma'aikata a jihar Taraba, na bin gwamna Darius Ishaku, bashin albashi a jihar.
Gwamna Ishaku zai miƙa mulki ne ga ɗan jam'iyyarsa, Agbu Kefas.
5. Bello Matawalle, jihar Zamfara
Yanzu haka ma'aikata a jihar Zamfara na bin gwamna Bello Matawalle, mai barin gado bashin albashin wata biyu.
Gwamnan na jam'iyyar APC da ya sha kashi a tazarcen da ya nema, zai miƙa ragamar mulkin jihar ga Dauda Lawal na jam'iyyar PDP, a ranar 29 ga watan Mayu.
6. Ben Ayade, jihar Cross River
Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River, bai biya ma'aikatan shara albashin wata huɗu ba.
Magajinsa, Bassey Otu, zai gamu da fushin ma'aikatan waɗanda a kwanan nan suka yi zanga-zanga kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu.
7. Nyesom Wike, jihar Rivers
Ana zargin gwamna Nyesom Wike, na jihar Rivers mai barin gado, ƙin biyan malaman makaranta da ke koyarwa a makarantun ƴaƴan malamai na makarantun gaba da sakandiren jihar, albashin shekara bakwai.
Wasu gamayyar ƙungiyoyi sun roƙi gwamnan da ya biya ma'aikatan haƙƙoƙinsu kafin ya sauka daga mulki.
Idan bai biya ba, nauyin biyan zai koma kan wanda zai gaje shi, Sim Fubara.
Tinubu Ba Zai Manta Ganduje, El-Rufai, Sauran Gwamnonin Arewa a Rabon Mukamai ba
A wani rahoton na daban kuma, wani na kusa da Bola Tinubu, ya bayyana cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, ba zai manta da gwamnonin Arewa wajen rabon muƙamai masu gwaɓi ba.
Bayo Onanuga, ya ce a kwanaki goma na farkon mulkin Tinubu, zai sanar da hadimansa.
Asali: Legit.ng