Majalisa: ‘Yan Takara 7 Sun Ayyana Matsaya, Sun Ki Yarda Ayi Zaman Sulhu da Shettima

Majalisa: ‘Yan Takara 7 Sun Ayyana Matsaya, Sun Ki Yarda Ayi Zaman Sulhu da Shettima

  • ‘Yan kungiyar G7 da ake kai ruwa rana da su a Jam’iyyar APC sun ki yin zama da Kashim Shettima
  • A wani jawabi da suka fitar, ‘Yan majalisar sun ce ana neman kakaba masu Hon. Abbass Tajudeen
  • Sanata Shettima bai samu damar zama da Wase, Betara, Jaji, Soli da sauran masu takarar majalisa ba

Abuja - Jam’iyyar APC ta gaza dinke barakar da ita a majalisa, Kashim Shettima bai iya yin zama da masu neman shugabancin majalisar wakilai ba.

A safiyar Asabar, Sun ta rahoto cewa ‘yan takaran da suka fito neman kujerar Femi Gbajabiamilla sun ki yarda su zauna da Sanata Kashim Shettima.

‘Yan majalisar da suka kafa kungiyar G7 sun ki amsa goron gayyatar Shettima, su ka ce ana kokarin tilasta masu goyon bayan Abbass Tajudeen ne.

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: Tsohon Gwamnan Arewa Mai Yakar APC Ya Yi Kus-Kus da Kwankwaso

Majalisa
'Yan majalisar wakilan Najeriya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

‘Yan G7 sun bayyana haka ne a wani jawabi da ya fito da Ahmed Idris Wase, Ado Doguwa, Mukhtar Betara da Yusuf Adamu Gagdi su ka sa hannu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sada Soli, Maryam Onuoha da Aminu Jaja duk sun rattaba hannunsu a jawabin da aka fitar.

Jawabin kungiyar G7

"‘Yan G7 sun samu labarin goron gayyatar da zababben mataimakin shugaban kasa, Mai girma Sanata Kashim Shettima ya aikawa zababbun ‘yan majalisa.
Mu na so mu sanar da zababbun ‘yan majalisa cewa Kashim Shettima bai aiko da gayyatar nan ba.
Hon. Tajudeen Abbas da masu tallata sa na shirin tara zababbun ‘yan majalisa zuwa wajen Shettima domin a nuna tamkar ya samu karbuwar da babu ita.

- 'Yan G7

Rahoton ya ce jawabin ya kare ne da nuna Wase da sauran ‘yan tafiyarsa, ba za su goyi bayan a kakaba masu shugabancin Tajudeen Abbas a majalisa ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisar Dattawa: Yari, Kalu da Musa Sun Kai Kokensu Wurin Adamu

This Day ta rahoto Hon. Muktar Betara Aliyu yana cewa daga cikinsu ne za a samu sabon shugaban majalisa, ya ce G7 za ta tsaida mutum guda ya yi takara.

Betara ya bayyana haka ne wajen kaddamar da yakin neman zaben Hon. Ahmed Wase a Abuja.

Shettima ya hadu da TJ

An ji labari tsohon Gwamnan ya nuna akwai hadari a samu wasu ‘yan majalisa da za su bijirewa umarnin jam’iyya kan tikitin Tajuddeen Abbas/Ben Kalu.

A gefe guda, Kashim Shettima ya tabbatar da ya na kokarin yin zama da sauran ‘yan takaran, ya ce sai da goyon bayan majalisa gwamnati za ta ci nasara.

Yayin da zababben shugaban Najeriya watau Bola Tinubu yake ketare, an samu rahoto cewa mataimakinsa ya na neman yadda zai daidaita abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng