Ya Zama Dole Na Zama Shugaban Ƙasa a Najeriya, Peter Obi
- Ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, ya ce ba makawa sai ya zama shugaban ƙasa a Najeriya ko ba yanzu ba
- Tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne a wurin taron kaddamar da littafinsa a Awka, babban birnin jihar Anambra ranar Jumu'a
- Ya ce ba wanda zasu yi jayayya da shi domin suna kaunar zaman lafiya kuma suna bin na gaba
Anambra - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party a babban zaben 2023, Peter Obi, ya ayyana cewa dole ne ya zama shugaban kasa a Najeriya.
Mista Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen shugaban kasa, ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da littafinsa mai suna, "Peter Obi: Many voices, one Perspectives”, a Awka, babban birnin jihar Anambra ranar Jumu'a.
Daily Trust ta rahoto cewa an shirya taron kaddamar da littafin ne da nufin tara kuɗin ɗaukar nauyin ƙarar da ya shigar gaban Kotun zaɓe, yana kalubalantar nasarar Bola Tinubu.
A kalamansa, Peter Obi ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Duk wanda ke tunanin zan sa kafa na bar ƙasar nan yana ɓata lokacinsa ne, ya zama dole na zama shugaban ƙasa a Najeriya, idan ba yau ba, nan gaba."
"Sauran masu son zama (shugaban kasa) su fito su gaya mana gaskiyar abinda suke fatan yi da kuma hanyar da zasu bi su aiwatar. Nan ƙasata ce, banda shaidar zama a wata ƙasa."
"Saboda haka dole na zama shugaban kasa, idan ba yanzu ba, nan gaba, ban ƙosa ba kuma ba sauri nake ba, na sadaukar da kaina domin ganin Najeriya ta gyaru."
Ba zami jayayya da kowa ba - Obi
Haka nan, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce zasu girmama duk hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a ƙarar da ake ci gaba da muhawara kanta.
The Cable ta rahoto Obi na cewa:
"Muna son zaman lafiya, ba wani ɗan siyasa da zamu yi jayayya da shi, kar guiwarku ta yi sanyi game da hakurin da nake baiwa wasu mutane. A matsayin matasa ba zamu yi faɗa da iyayenmu ba ko da kuwa muna kan gaskiya."
Mazauna Abuja Sun Maka Tinubu A Kotu
A wani labarin kuma Mazauna Abuja Sun Maka Tinubu A Kotu Don Hana Rantsar Da Shi a Ranar 29 ga watan Mayu, 2023
Wasu mutane 5 da suka kira kansu da 'yan Abuja masu rajistar katin zaɓe sun shigar da ƙara a gaban kotu, su na neman a dakatar da rantsar da Tinubu.
Asali: Legit.ng