Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa
- Akwai yiwuwar jam’iyyar APC NWC za ta canza tunani a kan shugabancin Majalisar Tarayya
- Wasu Sanatocin Arewa sun nuna sam ba za su goyi bayan yadda aka yi kason kujeru a Majalisa ba
- APC ta fara lallashin ‘Yan takararta, Shugaban jam’iyya na kasa ya hadu da wadanda aka fusata
Abuja - Wasu Sanatoci daga jihohin Arewa musamman wadanda aka zaba a APC sun yi barazanar juyawa jam’iyya baya a dalilin yadda aka yi rabon kujeru.
Rahoton Vanguard ya nuna Abdulaziz Yari da Sanatocin Arewacin kasar ba su gamsu da yadda jam’iyya mai mulki ta yi karon mukaman majalisar kasar ba.
Ganin halin da ake ciki, shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya shaida cewa jam’iyyarsa ta fara wasu zaman gaggawa domin dinke barakar da ke majalisa.
Yari da Wasu Fusatattun Sanatoci 3 Masu Neman Shugabancin Majalisa Sun Yi Kus-Kus da Shugabannin APC
Matsayar fustattun 'yan takara
A dalilin haka ne NWC tayi zama da Orji Kalu, Sani Musa, da Abdulaziz Yari. Na hudunsu, Osita Izunaso bai samu halartar taron sulhun da aka yi a jiya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Sanatan Zamfara, Abdulaziz Yari ya shaidawa jam’iyyarsa ta APC cewa dole abubuwa su sake zani, sauran zababbun Sanatoci su na tare da shi a nan.
Sanata Abdullahi Adamu ya lallabi fustatattun ‘yan takaran, amma kamar yadda Tribune ta fitar da rahoto, babu tabbacin zamansu ya kai ga haifar ‘da mai ido.
Kalu, Musa, Yari da Izunaso sun rubuta korafi ne ga APC NWC, su na masu nuna babu dalilin da za su yi biyayya ga tsarin da zai hana su yin takarar majalisa.
Sanatan Neja ta gabas, Sani Musa ya yi magana a madadin yankinsa, ya ce sun tallata APC a Arewa ta tsakiya duk da hadarin takarar Musulmi da Musulmi.
Sanatan ya soki matsayar jam’iyyarsa, ya ce akalla sai a zauna da su kafin a tsaida magana, an rahoto shi yana cewa ba za a kebe kujeru ga wasu daidaiku ba.
APC za ta duba lamarin
Da ya zanta da ‘yan jarida, Gwamna David Umahi ya shaida cewa APC NWC za ta sake duba yadda aka yi kason mukamai, ya nuna akwai gyara a lamarin.
Haka zalika shi ma Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma ya ce su na da yadda ake bi wajen ganin an magance sabani irin wanda aka samu a majalisa a yau.
Adamu ya fadawa wadanda ba su ji dadin yadda abubuwa su ke tafiya a APC ba, da su yi hakuri.
Sanatoci 18 sun ja daga
A wani rahoton dabam, an ji cewa Sanatoci 18 daga Arewa maso tsakiya ba su tare da jam’iyyar APC, sun zargi NWC da maida yankin na su saniyar ware a siyasa.
Haka lamarin yake a majalisar wakilan tarayya, ‘yan takara bakwai daga yankuna da-dama sun ce ba za su amince da tsarin kason mukaman da aka fito da shi ba.
Asali: Legit.ng