Ku Rungumi Kaddara, Basarake Ya Fadawa Masoyan Obi, Atiku, Su Bi Bayan Tinubu
- Mai martaba Sarkin Ife yana so a ajiye sabanin siyasa, a mara baya ga gwamnatin da za ta karbi mulki
- Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II ya yi kira ga wadanda suka goyi bayan PDP da LP a zaben 2023
- An gama zabe, Arole Oduduwa ya na so duk a hadu a goyi bayan Bola Tinubu domin ya gyara kasa
Lagos - Sarkin Ife Adeyeye Babatunde Enitan Ogunwusi Ojaja II (CFR) ya yi kira ga duka ‘Yan Najeriya da su goyi bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A rahoton Tribune, an ji Mai martaba Adeyeye Babatunde Enitan Ogunwusi Ojaja II ya na rokon a ajiye akidu na siyasa, a goyi bayan gwamnati mai zuwa.
Ooni ya yi wannan kira ne lokacin da ya karbi bakuncin wakilan da Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya aiko domin su ga shugaba mai jiran gado.
Tawagar da William Ruto ya aiko
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kenya, Francis Koskie da Alhaji Aliko Dangote da Harry Ebohen da Gwamna Dapo Abiodun su na cikin tawagar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
The Cable ta ce tattaunawar ta kunshi yadda Afrika za ta hada-kai musamman ta bangaren yarjejeniyar AfCFTA da za ta taimaka wajen kasuwanci.
"Har yanzu Najeriya ce kasa mafi karfin tattalin arziki, mai mafi yawan al’umma kuma gidan siyasa.
A ziyarar karshe da na kai, shugaban Kenya ya tabbatar mani da jajircewarsa wajen inganta daraja da kasuwancin kasarsa a Afrika.
Afrika ce kashin bayan karfin Duniya saboda haka dole mu canza salon arzikinmu kuma mu kare dukiyarmu mai tsawon tarihi."
- Oonin kasar Ife
Zaben 2023 ya wuce
"Yayin da ake shirin rantsar da shugaban kasa, ina kira gare mu duka, matasa da tsofaff, ‘Yan Obidients da Atikulates su ajiye kayan yakinsu.
Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
Babu dalilin tuna baya; daga yau sai kuma gobe. Lokaci ya yi da za mu rungumi sabaninmu. Mun sha bam-bam, amma burimu shi ne a gyara kasa.
Saboda haka mu hadu tare mu goyi bayan manufar Asiwaju Gbogbo Ile Oodua."
- Oonin kasar Ife
"Za mu bi bayan APC a majalisa"
An ji labari wakilan Jam’iyyun APC, PDP, da NNPP a karkashin jagorancin Hon. Usman Bello Kumo ba za su ja da Shugabannin Jam’iyyar APC a Majalisa ba.
Kumo, Hon. Kingsley Chinda, Aliyu Sani Madaki sun fitar da jawabi cewa sun shirya ajiye duk wata adawar siyasa, su yi aiki tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng