Tinubu, Atiku Da Obi: Abubuwa 5 Da Suka Wakana Yau A Kotun Sauraron Ƙarar Zaɓe

Tinubu, Atiku Da Obi: Abubuwa 5 Da Suka Wakana Yau A Kotun Sauraron Ƙarar Zaɓe

FCT, Abuja - A yau Litinin ne dai aka fara gudanar da shari'ar da aka daɗe ana ta jira ta ƙarar zaɓen shugaban ƙasa na zaɓen 2023 da ya gabata wata uku bayan gabatar da zaɓen.

'Yan takarar jam'iyun Adawa wato Atiku Abubakar na PDP da ya zo na biyu da kuma ɗan takarar jam'iyar Labour Peter Obi sunyi watsi da sakamakon zaɓen da INEC ta sanar na cewa Bola Tinubu ne ta lashe zaɓe.

Atiku Tinubu Obi
Atiku, Tinubu da Obi. Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Baya ga rashin karɓar sakamakon zaɓen, Atiku da Obi sun haɗa kai da wasu jam'iyyu uku na adawa wajen ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu wacce ta fara zamanta a yau Litinin.

Ga jerin abubuwan da suka wakana a yau ɗin:

Kotun ta yi fatali da koken da jam'iyyar AA ta shigar

Mai shari'a Haruna Tsammani ya yi fatali da ƙarar da jam'iyyar AA ta shigar na ƙalubalantar nasarar da Bola Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa na 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Kasa: Atiku Ya Ɗauki Manyan Lauyoyi 19 Don Kwace Nasara Daga Hannun Tinubu A Kotu, Jerin Sunaye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙalin ya yi watsi da shari'ar ne biyo bayan janyewa da jam'iyyar ta AA ta yi daga jerin masu shigar da ƙarar.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar Peter Obi

Kotun sauraron shari'ar ta ɗage sauraron ƙarar da Peter Obi da jam'iyyarsa ta Labour suka shigar na ƙalubalantar nasarar Tinubu Vanguard ta yi rahoto.

A kwanakin baya an zargi Peter Obi da abokin takarar shi Yusuf Datti Baba Ahmed da yunƙurin kawo tsaiko dangane da. batun rantsar da Tinubu da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar PDP da Atiku Abubakar

Haka nan ma dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta ɗage ƙarar da PDP da kuma ɗan takararta Atiku Abubakar suka shigar, tare da jam'iyyar APM suka shigar na ƙalubalantar zaɓen Tinubu zuwa Talata, 9 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Kori Karar Jam'iyya 1 Daga Cikin Waɗanda Suka Kalubalanci Nasarar Tinubu

Atiku dai shine wanda ya zo na biyu a zaɓen da ya gudana a watan Fabrairun shekarar 2023.

Kotu ta bawa masu ƙara shawarar su san abubuwan da zasu yi magana a kai

Domin a rage ɓata lokaci a yayin sauraron ƙarar, kotun ta buƙaci lauyoyin masu shigar ɗa ƙara akan su fahimci takamaiman abubuwan da za su yi magana akai domin gudun ƙara jawo tsaiko da kuma ɓata lokaci.

Masu zanga-zanga sun yi wa kotun tsinke

Wasu gungun masu zanga-zanga sun cika farfajiyar kotun inda suka kiraye ta da ta ɗage rantsar da Tinubu da ake shirin yi a ranar 29 ga watan nan.

Masu zanga-zangar dai sun ce akwai abubuwa da yawa da za su sanya a dakatar da rantsuwar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

APC ta bayyana sunayen waɗanda zasu jagoranci majisa

A yau Litinin ne dai jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da sunayen mutanen da zasu shugabanci majalisa ta goma. An bada sunan Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda zai shugabanci majisar dattawa.

Haka nan kuma, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC ɗin sun sanar da sunan Abbas Tajuddeen a matsayin wanda zai jagoranci majalisar dokoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel