Jigon Jam'iyyar APC Ya Bayyana Abu 1 Da Ka Iya Kawo Cikas Ga Rantsar Da Tinubu
- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, babu wani abu da zai kawo tangarɗa dangane da rantsar da shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu
- Mr. Williams Dakwom, wani mamba a majalisar yaƙin neman zaɓen APC a jihar Plateau, ya yi nuni da cewa jam'iyyar za ta mutunta doka sannan ta yi aiki da ita
- Yayin da ya ke sukar kalaman Onaiyekan, ya buƙaci faston da ya kai duk wani kokensa a gaban kotu, inda ya yi nuni da cewa itace kaɗai za ta iya hana rantsuwar
Jihar Plateau - Wani babban jigon jam'iyyar APC, ya yi fatali da kalaman da tsohon Akbishop na ɗariƙar Katolika a birnin tarayya Abuja, John Onaiyekan, ya yi kan cewa ba hankali a cikin rantsar da ƴan siyasar da ake ƙalubalantar nasararsu a kotu.
Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore
A wata tattaunawa da Legit.ng a ranar Litinin, 8 ga watan Mayu, Mr. Williams Dakwom, mamba a majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar Plateau, ya bayyana kalaman na Onaiyekan, a matsayin waɗanda ba su dace ba.
Jigon na APC, ya yi nuni da cewa kamata ya yi ya kai waɗannan kalaman ga hukumomin da suka dace, inda ya ƙara da cewa kotu ce kaɗai take da hurumin dakatar da rantsar da Tinubu, idan wani abu bai auku ba, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Waɗannan kalaman kamata ya yi ya kai su hukumomin da suka dace, idan bai gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen ba. Na tabbata ya san inda zai kai kokensa ba wai ya zo ya yi wani sakaran abu da ka iya kawo hargitsi a zaman lafiyar da mu ke samu ba."
"Saboda kotu ce kawai za ta iya hana rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ta, idan ba ita ba babu wanda ya isa ya hana mu karɓar ragamar mulkin ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023."
Jam'iyyar APC Ta Sanar Da Wadanda Za Su Shugabanci Majalisa Ta 10
A wani rahoton na daban kuma, jam'iyyar ta sanar da waɗanda ta ke son su zama shugabannin majalisa ta 10.
Jam'iyyar ta kai kujerar shugaban majalisar dattawa yankin Kudu maso Kudu, yankin Arewa maso Yamma, ya samu kujerar mataimakin majalisar dattawa da ta kakakin majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng