Akpabio/Barau: Abubuwan da Ya Dace a Sani Game da Sababbin Shugabannin Sanatoci

Akpabio/Barau: Abubuwan da Ya Dace a Sani Game da Sababbin Shugabannin Sanatoci

  • Sanata Godswill Akpabio ya zama sabon shugaban Majalisar Dattawa bayan zaben da aka shirya yau
  • Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa ya zama mataimakin shugaban majalisa ba tare da hamayya ba
  • Kafin samun wannan mukami, Sanata Akpabio ya taba zama Ministan tarayya da Gwamna a Akwa Ibom

Abuja - A rahoton nan, Legit.ng Hausa ta dauko maku tarihin Godswill Akpabio da kuma Barau Jibrin da su ka gaji Ahmad Lawan da Ovie Omo-Agege.

Haihuwa da makarantar Godswill Akpabio

A yau Godswill Obot Akpabio yana da shekaru 60 a Duniya, an haife shi ne a kauyen Ukana a garin Ikot Ntuen da ke karamar hukumar Essien Udim a Akwa Ibom.

Bayan rasuwar mahaifinsa, mahaifiyarsa Madam Lucy Obot Akpabio tayi kokari ya yi karatun sakandare a Fatakwal da digiri daga jami’ar Kalaba, ya zama Lauya.

Kara karanta wannan

Bayan Doke Yari, Sanata Akpabio Ya Karɓi Rantsuwa, Ya Kama Aiki Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Tun makaranta ya fara siyasa, da ya ke jami’a, Akpabio ya san yadda ya yi ya zama shugaban majalisar dalibai, kawunsa ya taba yin Ministan yankin Kudu maso gabas.

Da farko Akpabio ya fara ne a matsayin malamin makaranta, sai ya shiga aikin Lauya. Baya ga haka sai da ya zama Darekta a kamfanin EMIS Telecoms Ltd.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shiga siyasa da zama Gwamna

A 2002 ya shiga siyasa da Gwamna Obong Victor Attah ya nada shi Kwamishinan albarkatun mai. Kafin 2006, Akpabio ya rike ma’aikatu uku a Akwa Ibom.

Ganin ya zama Kwamishinan man fetur da kananan hukumomi da masarautu, na gidaje da filaye, sai ya nemi takarar Gwamna a 2007, kuma ya dace a PDP.

Zuwa 2011, mutanen Akwa Ibom su ka sake zaben Akpabio a kan mulki. Bayan shekaru biyu ya rike shugabancin kungiyar gwamnonin PDP da aka kafa.

Kara karanta wannan

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Zuwa Majalisar Dattawa a PDP

Da zai sauka daga mulki a 2015, sai Gwamnan ya nemi kujerar Sanatan Arewa maso yammacin jiharsa, ya sake galaba a PDP, ya zama shugaban marasa rinjaye.

Ana tafiya sai aka ji Sanatan ya bar PDP a 2018, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, amma ya gagara zarcewa. Hakan ya jawo aka nada shi Ministan Neja Delta.

Bayan shekaru uku yana Minista, Akpabio ya yi murabus, ya yi takarar shugaban kasa, a karshe ya janyewa Bola Tinubu, ya koma takarar majalisar dattawa.

Akpabio wanda ya samu goyon bayan APC da fadar shugaban kasa ya lashe zaben majalisa ta goma da kuri'a 63, shi kuma Abdulaziz Yari ya na da kuri'u 46.

Akpabio da Barau Jibrin
Godswill Akpabio da Barau Jibrin Hoto:@AdamuGarbaII
Asali: Twitter

Tashin Sanata Barau Jibrin

Barau mai shekaru 64 shi ne wanda APC ta ke so ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa, shi kadai ne Sanatan da ya tsallake guguwar NNPP a Kano.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalilai 5 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

An haifi Barau Ibrahim Jibrin a garin Kabo da ke jihar Kano, kuma a nan ya fara yin karatun boko. Daga baya ya digiri da digirgir a gida da New York a kasar Amurka.

‘Dan siyasar yana da shaidar digiri a ilmin Akanta da digiri na biyu a harkar tattalin arziki da kuma MBA, baya ga satifiket iri-iri da ya mallaka a wannan fanni.

A shekarar 1992 Barau ya bar aikin gwamnatin jihar Kano domin ya fara kasuwancin kansa, daga nan ya yi suna wajen kere-kere, gine-gine da harkar inshora.

'Dan kasuwa a siyasa

Bayan ya taba kasuwanci, a 1999 sai ‘dan kasuwan ya zama ‘dan majalisar Tarauni. Bayan shekaru a majalisar wakilai, ‘dan majalisar ya koma kasuwancinsa.

Daga baya aka dauko shi domin ba shi mukamai a gwamnatin gida da ta Olusegun Obasanjo. Barau ya samu takarar Sanata, amma na Arewacin Kano a 2015.

Daga Yunin 2015, Sanatan ya yi aiki a kwamitin man fetur, kasafin kudi, makarantun gaba da sakandare, Neja-Delta, masana’antu, sufurin kasa da sauransu.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Siyasar Barau tayi karfi

Bayanan da aka samu a shafinsa sun nuna ‘dan majalisar ne Sakataren Sanatocin jihohin Arewa.

Kamar yadda aka fi saninsa a mazabarsa, Maliya ya nemi takaran Gwamna a Kano a 2023, da ya rasa tikiti sai Dr. Abdullahi Ganduje ya bar masa kujerarsa.

A ranar 13 ga watan Yunin 2023, ya shiga ofis a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya bi sahun Salisu Buhari da Umar Ghali Na'Abba.

Jam'iyyar APC ta gama magana

A yammacin Litinin aka samu rahoto cewa jam'iyyar APC ta gamsu shugabannin majalisar dattawa su fito daga Arewa maso yamma da Kudu maso kudu.

Bayan an ware yankunan da za a kujerun, Jam’iyyar APC ta ayyana Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin wadanda ta ke goyon baya a takarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng