Zaɓen Shugaban Kasa: Atiku Ya Ɗauki Manyan Lauyoyi 19 Don Kwace Nasara Daga Hannun Tinubu A Kotu, Jerin Sunaye
- Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya ɗauki manyan lauyoyin da za su tunkari shari'ar da suke yi da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC
- Atikun ya ce ba wai domin kansa ko domin jam'iyyarsa ta PDP kawai yake fafutukar ba, yana ƙoƙarin kare dimokuraɗiyya ne
- Atiku da Peter Obi na jam'iyyar Labour sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen shugaban kasa sannan suka shigar da ƙara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe
Abuja - Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ɗauki hayar manyan lauyoyi guda 19 domin ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu.
Atikun dai ya zanta da lauyoyin nasa ne a ofishin yaƙin neman zaɓen shi da ke Abuja inda ya roƙe su akan su yi duk abinda ya kamata wajen ganin sun karɓo ma 'yan Najeriya haƙƙin su ICIR ta haƙaito.
Ba domin kaina kaɗai nake wannan fafutukar ba
Atiku ya kuma ƙara da cewar ya zama wajibi a garesu su bi waɗannan matakai ba wai domin iya kansa kaɗai ko don jam'iyyar PDP ba, sai dai domin kare mutuncin dimokuraɗiyya saboda 'yan baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lauyoyin waɗanda babban lauya JK Gadzama ke jagoranta sun haɗa da:
- Chris Uche
- Nuremi Jimoh
- Farfesa Maxwell Gidado
- Abdul Ibrahim
- Tayo Jegede
- Chukwuma Umeh
- Mahmood Magaji
- Paul Ogbole
- Goddy Uche
- Paul Usoro
- A.K Ajibade
- Nella Rabana
- Ken Mozia
- Mike Ozekhome
- Joe Abraham
- Emeka Etiaba
- Garba Tetengi
- O.M Atoyebi.
Atiku da Peter Obi sun ƙi yarda su karɓi faɗuwa
Har yanzu dai ɗan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour wato Peter Obi basu karɓi sakamakon zaɓen da aka ayyana Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara ba.
Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore
Jaridar Punch ta wallafa cewa 'yan takarar guda biyu sun ƙi amsa kiran da Bola Tinubu ya yi musu a lokacin da ya ke jawabin godiya, na cewar su zo a tafiyar da gwamnati tare.
Jam'iyyar AA ta janye kararta akan Tinubu
A zaman kotun da ake yi yau Litinin domin sauraren korafe-korafen da jam'iyyun da ba su gamsu da sakamakon zaben ba suka shigar, jam'yyar AA ta sanar da cewa ta janye kararta da ta shigar.
Jam'iyyar Action Alliance wato AA na daga cikin jam'iyyun da suka shigar da kara suna kalubalantar INEC kan sanar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a watan Fabrairun 2023.
Asali: Legit.ng