Batun Zama Shugaban Ma’aikata: El-Rufai Ya Tsefe Biri Har Wutsiya Game da Samun Matsayi a Mulkin Tinubu
- Gwamnan Kaduna, El-Rufai ya yi magana game da yanayin da yake ciki da kuma yadda ake yada jita-jita a kansa
- Ya ce bai da labarin za a bashi wata kujera a mulkin Tinubu, don haka a daina yada jita-jita game da hakan
- Ya kuma bayyana cewa, bayan mulkinsa, zai dauki hotuna ne kawai, amma zai ke ba gwamnoni shawari
Jihar Gombe - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa cewa yana neman zama shugaban ma’aikatan fadar zababben shugaban kasa Tinubu.
El-Rufai ya bayyana hakan ne ranar Asabar 6 ga watan Mayu a jihar Gombe a lokacin da yake zantawa da manema labarai, Daily Trust ta ruwaito.
Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, El-Rufai ya ziyarci jihar Gimbe domin kaddamar da shirin gidaje 550 da gwamnati ta gina da kuma cibiyar GOGIS.
Da Gaske El-Rufai Yana Zawarcin Kujerar Shugaban Ma'aikata a Gwamnatin Tinibu? Gwamnan Ya Fayyace Gaskiyar Lamari
Ya siffanta rahotannin da ake yadawa game da kujerun da ake tunanin bashi a matsayin zallar jita-jita da bata da wani tushe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zan ba da gudunmawa ta wasu hanyoyin
Gwamnan ya ce ya fi sha’awar bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya fiye da neman mukamai a halin da ake ciki.
El-Rufa’i ya bayyana cewa ba wai damawa dashi a gwamnati bane kadai hanyar da zai ba da gudummawa ga ci gaban Najeriya, yana mai cewa ko da ba ya cikin gwamnati, zai ci gaba da jajircewa wajen ganin kasar ta ci gaba.
A cewarsa:
"Ban yi wannan tattaunawa da zababben shugaban kasa ba kuma ba na son yin wani hasashe akai.
“Na karanta dukkan nau’in mukamai da ake cewa za a ba ni a jaridu amma ku sani, ni dan Najeriya ne mai kishin kasa.
“Ina son ganin kasata ta samu ci gaba kuma duk abin da zan iya don bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa, zan yi.
"Amma, ba dole ba ne in yi hakan a cikin gwamnati ba. Duk wanda ke aiki ko dai a kamfanoni masu zaman kansu ko kungiyoyin fararen hula yana ba da gudummawa.
"Babu wata hanya daya da za ace itace kawai na bayar da gudummawa ga kasar ba kuma ba zan daina yin aiki don ci gaban Najeriya ba."
Idan na sauka zan tafi hutun wani lokaci
Gwamnan ya ce, bayan sauka daga mulkin nan da kwanaki 22, zai dauki hutu amma zai ba da gudunmawarsa idan aka nemi shawarinsa a kowanne lokaci don ciyar da kasa gaba.
A cewarsa:
“Zan kasance a kamfani mai zaman kansa, ba wai shugaban ma’aikata ba. Zan dauki hutu sannan ba da shawari ga mutane irinsu gwamna Inuwa Yahaya idan suna bukata.”
Game da fara mulkin Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, El-Rufai ya ce ‘yan Najeriya ba za su yi dana-sanin zaban shugaban na APC ba.
Saura kwanaki kadan a rantsar da Tinubu, yana ci gaba da kulla alaka da gwamnonin Najeriya har da na PDP.
Asali: Legit.ng