Tinubu da APC Sun Yanke Wanda Zasu Shugabanci Majalisar Tarayya Ta 10
- Shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu, da jam'iyyar APC sun cimma matsaya kan raba muƙaman majalisar tarayya ta 10
- Sun aminta da Sanata Akpabio a mataayin shugaban majalisar dattawa da Tajudeen Abbas, a matsayin kakakin majalisar wakilai
- Haka zalika sun raba mukaman mataimakan shugabannin zuwa shiyyoyin arewa maso yamma da kudu maso gabas
Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki da zababben shugaban ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ka iya ɗaukar tsohon ministan Neja Delta, Godwill Akpabio, a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10.
Haka zalika jagororin APC da masu faɗa aji sun nuna goyon bayansu ga ɗan majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, a matsayin kakakin majalisar wakilan tarayya.
Jaridar Punch ta tattaro cewa wasu majiyoyi masu karfi, waɗanda suka halarci taron sirri da aka gudanar da gidan zababben shugaban kasa ranar Jumu'a ne suka tabbatar da haka.
Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya
Baya ga haka, wata majiya a majalisar tarayya ta ce har yanzun ba'a cimma matsaya kan kujerun mataimakin shugaban majalisar dattawa da mataimakin kakaki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan alama ce da ke nuna mai yuwuwa APC da shugaba mai jiran gado su bar kujerun mataimakan ga 'yan takara su fafata har a samu wanda ya samu nasara.
A wani sako da jaridar ta samu daga ɗaya daga ckin majiyoyin, ya ce:
"Zababben shugaban ƙasa da jam'iyyar APC sun aminta da cewa, kakakin majalisar wakilai ya fito daga arewa maso yamma; shugaban majalisar dattawa daga Kudu maso kudu."
"Tinubu da APC sun ɗauki Sanata Godwill Akpabio da Honorabul Tajudeen Abbas (Ph. D) a matsayin shugaban majalisar dattawa da kakaki majalisar wakilai bi da bi."
"Mataimakin shugaban majalisar dattawa zai fito daga arewa maso yamma sai kuma kudu maso gabashin Najeriya ta samu muƙamin mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya."
"An yanke matakin raba waɗannan muƙamai zuwa shiyyoyin nan ne a wurin taron da ya gudana yau (Jumu'a)," inji Majiyar, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Babu abinda zai faru, mun gama shiri - Rundunar soji
A wani labarin kuma Rundunar Soji Ya Magantu Kan Masu Shirin Hana Bikin Rantsar da Tinubu
Rundunar sojin Najeriya ta gargaɗi wasu yan siyasa da masu ruwa da tsaki, waɗanda ta ce sun shirin kawo hargitsi a bikin rantsar da sabon shugaban ƙasa.
Sojojin sun ce a shirye su ke zasu tari duk wanda ya zo da matsala a wannan rana, don haka ta shawarci duk mai hannu ya shiga taitayinsa.
Asali: Legit.ng