Buhari: Idan Matasa Sun Ga Babu Kan ta a Najeriya, Za Su Iya Tsallakawa Kasar Waje

Buhari: Idan Matasa Sun Ga Babu Kan ta a Najeriya, Za Su Iya Tsallakawa Kasar Waje

  • Shugaban Najeriya bai ga laifin wadanda suke barin Najeriya, su tafi neman kudi kasashen waje ba
  • Femi Adesina ya ce ya kan ba mutane shawarar tafiya ketare muddin za su samu aiki mai tsoka
  • Mai magana da yawun Shugaban kasar ya ce ci-rani ba laifi ba ne, halin da aka samu kai kenan

Abuja - Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Femi Adesina bai ganin cewa akwai wata matsala saboda mutane su na yin ci-rani.

Da aka zanta da shi a tashar talabijin Channels a ranar Alhamis, Mista Femi Adesina bai soki wadanda suka tsallaka zuwakasashen waje ba.

Hadimin Shugaban kasar yake cewa bai ga laifin mutane su bar Najeriya saboda halin rayuwa ba.

Femi Adesina yake cewa tun ba yau ba, an dade ana ci-ranin da aka fi sani da ‘Japa’ musamman a kudancin Najeriya, ya ce ba sabon abu ba ne.

Kara karanta wannan

Jirgin saman NigeriaAir Zai Fara Tashi Kafin Shugaba Buhari Ya Bar Aso Rock – Minista

Babu yadda aka iya

Daily Trust ta rahoto Adesina yana mai cewa zama a Najeriyar shi ne abin da ya dace, amma akwai lokutanta da akasin hakan ne yake faruwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari
Muhammadu Buhari da kayan Sojoji Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

"Lamarin ‘Japa’ ba yau aka fara ba, dama tun can yana nan. Babu wani laifi saboda mutane sun tafi kasar waje.
Idan ku na tunanin za ku fi samun dama a ketare, ko ta wani hali ne, ku tafi. Ba laifi ba ne.
Abin da ya dace shi ne a tsaya a taimaki Najeriya, amma mun san ba duk abin da ya dace ne yake faruwa a ko yaushe ba.
Saboda haka dole mu hakura da halin da muka samu kan mu.

- Femi Adesina

Jaridar The Cable da ta bibiyi hirar, ta ce Mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya nuna bai adawa ga wadanda suke barin gidajensu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Ku bar Najeriya idan... - Adesina

“Ina fadawa matasa idan sun samu damar fita ketare, ba damar yin kananan ayyukan da za a iya a Najeriya ba, to su tafi.
Nan gaba za ku samu cigaba a rayuwa, ku sake dawowa ku taimaki tattalin arzikin kasar nan.

- Femi Adesina

Buhari da Gwamnoni

A yammacin Alhamis aka ji labari Muhammadu Buhari ya ware Gwamnonin Kano da Kaduna, ya yaba masu a lokacin da aka kai masa ziyara.

Shugaba mai barin gado ya bayyana cewa Kaduna ne garin da zai koma zama idan ya bar Aso Rock, kafin nan zai shafe watanni shida a Daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel