Atiku, Tinubu, Obi: Satguru Maharaj Ji Ya Bada Sabuwar 'Wahayi' Game Da Makomar Zaben 2023
- Shugaban One Love Family, Satguru Maharaj Ji, ya magantu game da sakamakon zaben 2023 da Bola Tinubu ya lashe
- Malamin ya kuma yi hasashen cewa mulkin Tinubu zai zama wani mataki na samar da kyakkyawar gwamnati a Najeriya saboda kwarewarsa
- Guru ya bayyana cewa zabar Peter Obi na jam'iyyar LP zai taimaka wa masu fafutukar kafa Biafra yayin da shi kuma Atiku bai cancanci shugabancin Najeriya ba
Ibadan, Oyo - Satguru Maharaj Ji, shugaban One Love Family, ya ce zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, na da "kwarewar da zai gudanar da kyakkyawar gwamnati a Najeriya."
Malamin ya bayyana haka lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai ranar Lahadi, 23 ga Afrilu, a bikin murnar kasacewarsa cikakken jagora, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abin Da Satguru Maharaj Ji Ya Hango Kan Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi
A cewar Guru, Tinubu mutum ne mai kwarewar da zai iya saita al'amura a Najeriya. Ya ce Tinubu zai iya "ciyar da kasar gaba ta hanyar amfani da arzikin da kasar ke da shi yadda zata iya gogayya da sauran kasashen duniya."
Da ya ke maganar Peter Obi, dan takarar LP a zaben 2023, malamin ya jaddada cewa zabar tsohon gwamnan Anambra tamkar ''taimaka wa Biafra ne''.
Ya cigaba da cewa Atiku Abubakar bai cancanci mulkin Najeriya ba saboda ya karya dokar jam'iyyarsa, PDP kuma ya na son zama shugaban Najeriya ba tare da amincewa da tsarin karba karba ba sannan ya watsar da gwamnoni.
Zazzafan labari game da Satguru Ji, Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi, zaben 2023, APC, PDP
Ya ce:
"Shi (Atiku) ba shine Najeriya ba, Najeriya tafi shi. Ya karya doka."
Malamin addinin ya bukaci yan adawar Tinubu, ciki har da Atiku na jam'iyyar PDP da Obi, da su janye batun kalubalantar nasarar Tinubu a kotu.
Guru ya kuma yi sharhi kan tikitin Muslim-Muslim na jam'iyyar APC in da ya bukaci jam'iyyar tayi watsi da addini wajen zabar shugaban majalisar dattawa.
Tinubu ya dawo Najeriya a shirye shiryen rantsuwa ranar 29 ga watan Mayu
A baya bayan nan Legit.ng ta ruwaito zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya dawo Najeriya bayan shafe sama da kwanaki 30 a kasar Faransa don hutawa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2023.
Tinubu ya bar Najeriya ranar Talata, 21 ga Maris, don yin hutu a kasar Faransa bayan gudanar da yakin neman zabe kafin gudanar da babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng