Yadda Aka Raba Kujerun Majalisar Dokoki Tsakanin Jam’iyyun NNPP da APC a Kano

Yadda Aka Raba Kujerun Majalisar Dokoki Tsakanin Jam’iyyun NNPP da APC a Kano

  • A 2023, Jam’iyyar NNPP za ta karbi rinjayen da APC ta ke da ita a Majalisar dokokin jihar Kano
  • Sakamakon zaben da hukumar INEC ta karasa ya nuna Jam’iyya mai mulki ta na da kujeru 14 ne
  • NNPP ta samu ‘Yan majalisar jiha 26, Jam’iyyar adawa ta PDP ba ta samu ko ‘Dan majalisa 1 ba

Kano - Bayan zaben 2023 da aka karasa a jihar Kano, jam’iyyar NNPP mai hamayya ta mallaki rinjaye a majalisar dokoki, ta na da ‘yan majalisu 26.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa jam’iyya mai alamar kayan marmari za ta karbe iko da majalisar jihar Kano da za a rantsar a watan Yunin 2023.

Daga wadanda aka ba takardar shaidar cin zabe, an fahimci APC da take da rinjaye a yanzu, ta tashi ne da ‘yan majalisar dokoki 14 a karshen zabukan.

Kara karanta wannan

Ba Za Mu Yarda ba: PDP Ta Garzaya Kotu Bayan APC Ta Ci Gwamna da Kuri’u 40, 000

Jam’iyyar NNPP ta samu gagarumar nasara musamman a kananan hukumomin da ke cikin birnin Kano. PDP ba ta tashi da kujeru ko guda a cikin 40 ba.

NNPP ta yi galaba a kan APC

Kujerun da ‘yan takaran NNPP suka lashe a zaben ‘yan majalisar Jiha sun hada da; Ajingi, Gabasawa, Wudil, Rimin Gado/Tofa, sai Dala, da na Fagge.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Yan NNPP za su wakilci mazabun Nasarawa, Sumaila, Gwale, Madobi, Bebeji, Kura/Garun Malam, Kiru, Kumbotso, Tarauni, Rogo da kuma Karaye.

NNPP a Kano
Zababbun 'Yan majalisa a NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Jam’iyyar ta ci Bunkure, Rano, Kibiya, Ungogo, Garko, Dawakin Kudu, Minjibir, Albasu da Birni.

APC ta na da Arewacin Kano

Legit.ng Hausa ta fahimci APC mai rinjaye da mulki a yau ta fi yin galaba ne a bangaren Arewacin jihar Kano, sannan ta samu wasu kujeru a Kudu.

Warawa, Bichi, Bagwai/Shanono, Tsanyawa/Kunci, Takai, Gezawa, Kabo, Gwarzo, Danbatta, Makoda, Dawakin Tofa, da Gaya sun fada hannun NNPP.

Kara karanta wannan

Magana Ta Koma Kotu, Binani Ta Nemi a Tsaida Tattara Sakamakon Zaben Adamawa

Jam’iyyar APC ta samu ‘yan majalisun dokoki da za su wakilci Tudunwada da Doguwa.

Kamar yadda rahoton ya zo, babban jami’in hukumar zabe, Zango Abdu ya yi farin ciki da sakamakon, yake cewa sun shirya zabuka na kwarai a 2023.

Afuwar Gwamna Ganduje

An ji labari Injiniya Muazu Magaji wanda ya fito daga yanki daya da Abdullahi Ganduje yana da ta-cewa bayan Mai girma Gwamna ya nemi a yafe masa.

Dr. Abdullahi Ganduje ya kori Dansarauniya daga aiki har sau biyu, da farko a dalilin Abba Kyari, ‘dan siyasar ya ce ya yafe, amma fa ba zai manta da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng