Ba Za Mu Yarda ba: PDP Ta Garzaya Kotu Bayan APC Ta Ci Gwamna da Kuri’u 40, 000
- A zaben Gwamna da aka yi a jihar Kebbi, Dan takarar jam’iyyar PDP bai yarda APC ta doke shi ba
- Janar Aminu Bande ya shaidawa masoyansa cewa za su dauki lauyoyi domin su tafi kotun karar zabe
- Nasiru Idris ya zama zababben Gwamna a APC, Bande wanda ya samu kuri’u 360,940 yana da ja
Kebbi - ‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben sabon Gwamnan jihar Kebbi, Aminu Bande, bai amince da nasarar da APC mai-ci ta samu ba.
Janar Aminu Bande mai ritaya zai tafi kotun zabe domin kalubalantar nasarar Nasiru Idris da jam’iyyarsa ta APC, Punch ce ta fitar da rahoton.
Hukumar INEC mai zaman kan ta bakin Farfesa Saidu Yusuf, ta sanar da Kauran Gwandu a matsayin wanda ya zo na farko a zaben Gwamnan.
Farfesa Saidu Yusuf ya ce jam’iyyar APC ta samu kuri’u 409,225, sai PDP tana biye da 360,940.
Za a hadu a kotun zabe
Da yake magana da manema labarai a garin Birnin Kebbi, Bande ya ce shi da jam’iyyar PDP za su je kotu domin karbe nasarar su da aka ba APC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon sojan ya nuna kotu za ta iya tabbatar da kuri’un da aka kadawa PDP a zaben da aka yi, a cewarsa su ne asalin wadanda suka yi galaba a takarar.
New Telegraph ta rahoto Janar din yana cewa kotun sauraron karar zaben Gwamna a Kebbi za ta ba PDP nasara domin ita ta fi samun kuri’u.
An cafke wasu 'yan jam’iyyar adawa
A karshe, ‘dan takaran ya zargi Gwamnatin Atiku Abubakar Bagudu da kama wasu ‘ya ‘yan PDP, ya bukaci a gaggauta fito da su daga kurkuku.
Ina godewa duka magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da suka tsaya mani a wannan gwagwarmyar, saboda haka ba za mu ba su kunya ba.
Domin za mu bi duk hanyar da za mu iya a shari’a domin karbo nasarar da muka samu.
Yayin da mu ke kira ga magoya bayanmu da za su zama masu bin doka da oda...
...mu na kira ga gwamnatin Jiha ta fito da magoya bayanmu fiye da 60 da ke tsare a gidajen gyaran hali ba tare da dalili ba.
- Aminu Bande
Zaben majalisar dattawa
Rahoton da ya zo a ranar Talata shi ne Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma, Danladi Sankara ya fadi wanda ya dace ya rike Majalisa.
Takarar Barau Jibrin ta samu kwarin gwiwa duk da Sanatan APC bai cikin wadanda za su zabe shi, shi ma Masud El-Jibrin a kan haka yake.
Asali: Legit.ng