Ana Dab Da Rantsuwa, An Bankado Wani Laifin Tinubu Da Ka Iya Hana a Rantsar Da Shi

Ana Dab Da Rantsuwa, An Bankado Wani Laifin Tinubu Da Ka Iya Hana a Rantsar Da Shi

  • An nemi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya fayyace gaskiya kan wani fasfo da ke yawo wanda ya nuna shi a matsayin ɗan ƙasar Guinea Conakry
  • Wata ƙungiyar magoya baya ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, mai suna Peter Obi Support Network (POSN), itace ta yi wannan kiran
  • Obi yayi watsi da sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa inda yayi zargin cewa an masa maguɗi sannan zai tabbatar a kotu cewa shi ya lashe zaɓen

Awka, Anambra - Ƙungiyar Peter Obi Support Network (POSN), ta buƙaci ɗan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), da ya fayyace gaskiya kan zargin cewa shi ɗan ƙasa biyu ne.

New Telegraph tace ƙungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 17 ga watan Afirilu, inda ta ƙara da cewa dole ne Tinubu ya wanke kan sa kan batun da yake yawo a soshiyal midiya ana zargin sa da ɓoye cewa yana da ikon zama ɗan ƙasa a ƙasar Guinea.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rayuka Da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Rikici Tsakanin Makiyaya Da Manoma a Jihar Arewa

An nemi Tinubu ya bayyana gaskiya kan zaman sa dan kasar Guinea
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Peter Obi Hoto: Bola Tinubu, Peter Obi
Asali: Twitter

Wakilin Legit.ng a Anambra, Mokwugwo Solomon, ya hakaito cewa wani hoton fasfo na ƙasar Guinea, mallakin Bola Tinubu, ya karaɗe shafukan yanar gizo bayan wani ɗan jaridan yanar gizo, David Hundeyin, ya sanya shi a Twitter.

A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar ya rattaɓawa hannu, Onwuasoanya Jones, yayi nuni da cewa shugabancin Tinubu na fuskantar babban haɗari saboda dokokin ƙasar nan sun samar da matsaya akan zama ɗan ƙasa biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hankalin mu ya kai kan wani fasfon ƙasar Guinea Conakry na Bola Tinubu, wanda ya yaɗu a yanar gizo bayan ɗan jarida, David Hundeyin, ya sanya kwafin sa a shafin sa na Twitter."
"Kowa yana sane da irin kyakkyawar alaƙar da ke a tsakanin shubagan ƙasar Guinea, Alhpa Conde, da Tinubu, inda har Tinubu ya taɓa bayyana cewa ya taimakawa Conde yin tazarce a Oktoban 2015."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Sanya Baki a Rikicin Sudan, Ya Aike Da Wani Muhimman Sako

Ƙungiyar POSN ta ci gaba da cewa:

"Zargin zama ɗan ƙasa biyu da ake yiwa Tinubu ya sanya akwai buƙatar a binciki tsohon gwamnan jihar Legas kan zargin yin rantsuwa bisa ƙarya."
"Tinubu bai bayyana komai ba dangane da zaman sa ɗan ƙasar Guinea a takardun da ya miƙa wa INEC domin zaɓen shugaban ƙasan Najeriya."
"Da zargin zama ɗan ƙasa biyu da ake yi wa Tinubu, yana da kyau a gare shi ya yi martani kan zargin saboda duk wani mai riƙe da kujerar siyasa mai halaccin zama ɗan wata ƙasar, ka iya rasa kujerar sa kamar yadda dokokin tarayyar Najeriya suka yi tanadi."
"Tinubu yana buƙatar ya hanzarta da gaggawa ya fito ya fayyace gaskiya kan wannan zargin, wanda yake zama babbar barazana ga kujerar shugabancin ƙasan da INEC tace ya lashe."

Magana Ta Koma Kotu, Binani Ta Nemi a Tsaida Tattara Sakamakon Zaben Adamawa

A wani labarin na daban kuma, Aisha Binani ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta nufi gaban kotu da wata buƙata.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zabe, PDP Ta Bankado Shirin Yi Wa Dan Takarar Gwamnanta Magudi a Adamawa

Ƴar takarar tana neman kotun da ta hana hukumar INEC ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng