Atiku, Obi da Kwankwaso Sun Taimaka Tinubu Ya Samu Nasara, Fashola

Atiku, Obi da Kwankwaso Sun Taimaka Tinubu Ya Samu Nasara, Fashola

  • Ministan ayyuka da gidaje ya yi ikirarin cewa manyan yan takarar tsagin adawa da kansu suka taimaka wa Bola Tinubu
  • Babatunde Fashola ya ce Atiku, Obi da Kwankwaso yan gida ɗaya ne a zaben 2019 amma kafin 2023 kowa ya kama gabansa
  • A cewar tsohon gwamnan siyasa yar lissafi ce idan baka iya buga wa daidai ba, to ba zaka kai labari ba

Abuja - Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana ra'ayinsa cewa manyan 'yan takarar shugaban kasa na tsagin adawa sun tallafa wajen samun nasarar Bola Tinubu.

Ministan ya yi wannan furucin ne yayin da ya bayyana a cikin shirin Politics Today na Channels tv ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu, 2023.

Manyan yan takarar shugaban kasa hudu.
Atiku, Obi da Kwankwaso Sun Taimaka Tinubu Ya Samu Nasara, Fashola Hoto: channelstv
Asali: UGC

Fashola ya ce Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da Rabiu Kwankwaso na NNPP da kansu suka miƙa wa Bola Tinubu tikitin nasara lokacin da suka gaza haɗa kai wuri ɗaya.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jerin 'yan takarar da suka yi nasara a zaben jiya Asabar

A zaɓen shugaban kasan da aka kammala ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, Tinubu ya samu kuri'u 8,794,726, ya tumurmusa Atiku Abubakar na PDP, wanda ya tashi da kuri'u 6,984,520.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ɗan takara a inuwar Labour Party, Peter Obi, ya zo na uku da kuri'u 6,101,533 yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ya samu kuri'a 1,496,687 a babban zaɓen 2023.

Yadda manyan yan takarar suka taimaka wa Tinubu

Fashola, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce manyan 'yan takarar guda uku sun raba gari daga jam'iyyar PDP bayan zaɓen shugaban ƙasan 2019, wanda ya sauƙaƙa wa Tinubu lashe zaɓe a 2023.

A rahoto The Nation, Ministan ya ce:

"Siyasa wasan lambobi ne kuma lambobin suna da alamun lissafi, akwai tarawa da nunkawa. Jam'iyyar APC tana tarawa kuma ta nunka. Alal misali wasu gwamnonin PDP kamar na Kuros Riba, Zamfara da Ebonyi sun shigo APC."

Kara karanta wannan

Cikon Zaɓe: Jam'iyyar APC Ta Ƙara Lashe Zaben Sanata a Arewacin Najeriya

"Ita kuma PDP rabawa take da ɗebewa, saboda haka manyan yan takara uku da suka gwabza da mu, PDP, LP da NNPP, yan gida ɗaya ne watau PDP a 2019, duk da haka suka rasa kusan kuri'u miliyan huɗu."
"Yanzu kuma sun raba wannan tikicin gida uku, taya zasu iya kai labari? Don haka da kansu suka watsar da nasararsu ta hanyar raba karfinsu. Bayan haka kuma aka ɗebe gwamnonin G-5."

APC ta kara samun nasara a Kebbi

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Yan Majalisu 8 a Cikon Zaben Jihar Kebbi

Hukumar INEC ta bayyana 'yan takarar jam'iyyar APC a matsayin wadanda suka ci zabe a mazabun mambobin majalisar dokokin Kebbi guda 8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262