IRev Ta Tona Magudi da Aka Shirya Domin APC da Tinubu Su Ci Zaben Jihar Ribas

IRev Ta Tona Magudi da Aka Shirya Domin APC da Tinubu Su Ci Zaben Jihar Ribas

  • Alamu na Jam’iyyar LP ta yi nasara a zaben Shugaban kasar 2023 a Ribas, ba APC mai mulki ba
  • Shafin IRev ya nuna a asalin kuri’un da mutane suka kada, Peter Obi yana gaban Bola Tinubu
  • Da aka tashi sanar da sakamakon zabe, Hukumar INEC ta ce jam’iyyar APC ta zo farko, sannan LP

Rivers - Jam’iyyar LP da ‘dan takaranta a zaben shugaban kasa da aka yi a bana, Peter Obi ne suka yi nasara a jihar Ribas ba Asiwaju Bola Tinubu ba.

Premium Times ta bi diddikin sakamakon zaben da aka daura a kan shafin IRev da hukumar INEC ta fito da shi, an tabbatar da cewa an shirya magudi.

Sakamakon zaben karamar hukumar Obio/Akpor da ke kan shafin yanar gizon ya nuna Peter Obi ne ‘dan takaran da ya fi yawan kuri’u, ba na APC ba.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jerin 'yan takarar da suka yi nasara a zaben jiya Asabar

A wannan yanki, hukumar INEC ta sanar da cewa Bola Tinubu yana da kuri’u 80, 239 yayin da Obi ya kare da 2, 829, jaridar ta ce sam ba haka abin yake ba.

Meya faru a Mahaifar Gwamna, Obio/Akpor?

Sakamakon da aka samu na mazabu 17 da ke Obio/Akpor daga IRev sun nuna abin da INEC ta sanar ya sha bam-bam da abin da mutane suka kada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da aka iya gano cewa a rumfuna 1, 211, mutane 17, 158 suka zabi jam’iyyar APC, LP kuwa ta na da kuri’u 73,311, hakan ya nuna Obi ya yi nasara.

Tinubu
Bola Tinubu a jirgi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar ta yi binciken ne a rumfuna fiye da 1, 000, wanda ya kai 94.13%. Har yanzu akwai sakamakon da ba su kan shafin ko wasu ba za su karantu ba.

Kara karanta wannan

Zaben yau Asabar: Mata sun tona asirin APC a jihar Arewa, sun fadi yadda ake ba su kudi

Binciken ya nuna akwai inda aka yi murdiya karara ta hanyar canza sakamakon zaben. Alal misali, a haka APC ta samu nasara a Oro-Igwe a Rumuorluoji.

An rika canza sakamako da hannu

Akwai inda jam’iyyar APC ta samu kuri’u 17, amma sai aka maida sakamakon ya zama 217, ita kuwa LP mai 227, sai ta kare da 027 a wannan akwati.

A mazabar Rumuokoro, an rika daukar kuri’un Peter Obi, ana mallakawa ‘dan takaran APC. Wasu wuraren an yi amfani da kuri’un zaben ‘yan majalisa ne.

Da farko jam’iyyar LP ce kan gaba da ake tattara sakamakon zaben, sai APC ta na biye – kuri’u 169,414 da 148,979, kafin a ce kobo, sai aka ji labari ya canza.

Jam’iyyar APC ta samu tulin kuri’u ne daga mahaifar Gwamna Nyesom Wike, Obio/Akpor da Degema inda a nan ma aka gano an hada da 'yar coge.

Zaben shugaban majalisa

Tun da an zabi Bola Tinubu da Kashim Shettima, an ji labari Sanatan Imo, Osita Izunaso yana burin shugaban majalisar dattawa a zaben da za ayi.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ambato Mutum 2 da Suka Hana Atiku Zama Shugaban Najeriya

Shekaru 20 da suka wuce Izunaso ya zama ‘dan majalisa, ganin shi Ibo ne, ya ce baya ga ya san kan majalisa, nasararsa za ta kawo zaman lafiya a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng