Jerin Jihohi 23 da Duka Mazabun da INEC Za Ta Karasa Gudanar da Zabe a Makon Nan
FCT, Abuja - Hukumar INEC mai zaman kan ta, za ta shirya zabuka a wasu jihohi akalla 24 a karshen makon nan bayan an gagara kammala su a tashin farko.
Legit.ng ta tattaro wuraren da ake sa ran zabuka za su kankama a ranar Asabar a Najeriya.
Hankalin mutane ya fi tattara zuwa ga zaben Gwamnonin jihohin da za a kammala a jihohin Adamawa da Kebbi, inda ba a san wanda ya yi nasara ba.
Baya ga zaben Gwamnoni, akwai na majalisar wakilan tarayya da na Sanatoci, nan da ‘yan kwanaki ake sa ran kowane mai takara zai san makomarsa.
Zaben Gwamnoni
- Adamawa
- Kebbi
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Akwai kananan hukumomi 21 da za a shirya zabuka a Adamawa da Kebbi, a wadannan kananan hukumomi, za a kada kuri’u a rumfuna 69 a Adamawa.
Ana Saura Awanni 24: Atiku Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Game da Cikon Zaɓen Gwamna a Adamawa da Kebbi
Haka zalika Hukumar INEC ta kasa za ta kammala zaben rumfuna 142 na jihar Kebbi a gobe. Ana fafatawa ne tsakanin jam’iyyun PDP da kuma APC mai mulki.
Makomar Aisha Dahiru Binani da Gwamna Umaru Ahmadu Fintiri ya na hannun kuri’u 36,935 da za a kada, a jihar Kebbi kuwa mutane 94,209 za suyi zabe.
Takarar Sanatoci
Akwai jihohin Arewa 3 da za a kammala zaben majalisar dattawa, su ne:
1. Sokoto
2. Zamfara
3. Kebbi
Za a sake sabon zabe a mazabun Sokoto na Arewa, Gabas, da Kudu. Zabuka za su gudanar a kananan hukumomi 23, mutum 227, 743 suka yi rajista a rumfuna 389.
A yankin Kebbi ta Arewa ta Zamfara ta tsakiya za ayi zaben Sanata. Zaben za su shafi rumfunan Kebbi ta Arewa 23 da kuma wasu 83 da ke Zamfara ta tsakiya.
Majalisar Wakilan Tarayya
Zaben ‘yan majalisar wakilai da za ayi zai shafi jihohi da-dama, su ne:
1. Anambra 1
2. Bayelsa 1
3. Rivers II
4. Sokoto II
5. Kano II
6. Akwa Ibom II
7. Oyo II
8. Taraba I
9. Imo I
10. Kebbi I
11. Ebonyi I
12. Jigawa I
13. Zamfara II
14. Edo I
15. Kogi I.
Bola Tinubu ga Atiku Abubakar
Da aka je kotun sauraron karar zaben bana, Shugaba mai jiran gado ya maidawa PDP martani, ya fada masa Jam’iyyun LP da NNPP suka kwashe maka kuri’u.
An ji labari Bola Tinubu ya ce a 2019, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su na nan a jam’iyyar PDP, wannan karo sun hana jam’iyyar samun kuri’u miliyan 7.5.
Asali: Legit.ng