Zababben Shugaban Kasa, Tinubu Ya Shiga Cikin Mutum 100 da Suka Fi Tasiri a Duniya
- Lashe zaben Najeriya da Asiwaju Bola Tinubu ya yi, ya jawo mujallar nan ta TIME ta jinjina masa
- Da aka tashi jero sunayen mutum 100 da tasirinsu ya kai inda ya kai a ban kasa, an kawo Bola Tinubu
- TIME ta ce zababben shugaban na Najeriya ya kama hanyar yin mulki bayan shekaru 20 yana shiri
United States - A cikin mutum 100 da ake tunanin sun fi kowa tasiri yanzu a Duniya, akwai zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu.
A shekara 71, Asiwaju Bola Tinubu ya shiga sahun mutum 100 da Duniya ta yarda da karfi da tasirinsu, mujallar TIME ta Amurka ta jero har da sunansa.
Daga cikin shugabannin kasashe 20 da suka shiga wannan sahu a shekarar nan ta 2023, Premium Times ta ce akwai wanda ya lashe zaben Najeriya.
Mujallar kasar Amurkan ta ce Bola Tinubu ya yi abin da sai wane-da wane bayan lashe zaben sabon shugaban da aka yi a Najeriya a farkon shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Time ta ce ‘dan takaran na jam’iyya mai-ci ya samu nasara ne bayan tanadin shekaru. Tribune ta ce an jero kalubalen da ke gaban mai jiran gadon.
"Lashe zabe a kasar da ta fi kowa yawan mutane a Afrika ba abu ne mai sauki ba. Amma Bola Ahmed Tinubu ya samu kusan shekaru 20 yana shiri.
Magoya bayansa su na kiransa Jagaban watau Shugaban Dakaru, a karon farko a watan Maris, mai shekara 71 a Duniyan ya tsaya takarar shugaban kasa.
Taken kamfen dinsa shi ne “Yanzu lokaci na ne”, hakan yana nuni ga tsawon shekarun da ya dauka a matsayin mai daura mutane a kan mulki.
- TIME
Tinubu ya bar tarihi a Duniya
Wannan ne shekara ta 20 da mujallar tayi ta na tattaro sunayen mutanen da suka yi fice a bangarori dabam-dabam a Duniya, ‘yan Najeriya su kan samu shiga.
Rahoton ya ce a baya an samu sunayen mutane irinsu Shugaba Muhammadu Buhari, Ngozi Okonjo-Iweala, Tony Elumelu da irinsu Chimamanda Adichie.
Sunayen ya kan kunshi ‘yan siyasa da masu rike mukaman gwamnati, attajirai da masana.
Za a rantsar da Musulmi da Musulmi
Musulmai biyu za a rantsar a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa a ranar 29 ga watan Mayu a sakamakon nasarar Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Ganin haka ne aka ji labari wani Shugaba a jam'iyyar APC mai mulki, Salihu Lukman bai goyon bayan wani Musulmin ya zama shugaban majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng