“Kana Jin Haushi Ne Don Na Ki Goyon Bayan Kudirinka Na Son Zama Magajin Buhari”, Dino Ga Wike
- Sanata Dino Melaye ya mayar da martani ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas kan furucin da ya yi game da takararsa na son zama gwamnan jihar Kogi
- Tsohon dan majalisar tarayyar ya ce ba komai ke damun Wike ba face mara masa baya da bai yi ba a kokarinsa na son mallakar tikitin shugbana kasa na PDP a 2023
- Milaye ya ce abun da ya kamata gwamnan na Ribas ya fi mayar da hankali a kai yanzu shine yadda zai yi rayuwa bayan ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu
Mai neman takarar gwamnan jihar Kogi karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Dino Melaye, ya caccaki gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike saboda furucin da ya yi a kansa a baya-bayan nan.
Jaridar Daily Post ta rahoto cewa Gwamna Wike wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Port Harcourt ya ce tsohon dan majalisar bai cancanci zama gwamnan jihar Kogi ba.
Da yake martani a wata sanarwa a ranar Talata, Dino ya ce rikicinsa da Wike ya samo asali ne saboda ya ki marawa kudirin gwamnan na son zama shugaban kasa baya.
Ni ba Atiku bane da ya kyale ka, Dino ga Wike
Dino ya ce kamata ya yi ace Wike ya dunga shirya yadda zai yi rayuwa bayan ya bar gidan gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Na fahimci abun da ke yi wa Wike ciwo. Ya so na marawa kudirinsa mara fa'ida na son zama dan takarar shugaban kasa na PDP baya a zaben 2023 amma ganin cewa bai cancanci tikitin ba, sai na marawa mai girma Atiku Abubakar, kwararre kuma hazikin dan kasa wanda ya yi watsi da duk wani soki-burudun Wike a lokacin zaben baya.
"Watakila Wike ya zata ni Mai Girma Atiku Abubakar ne. Ya kamata ya gode cewa yanzu da ya tabo wutsiyar damisa da katse masa bacci, ya tara ya samu."
Dino Melaye dai ya ayyana aniyarsa na son takarar kujerar gwamnan jihar Kogi wanda za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
PDP ba za ta kai labari ba a zaben gwamnan Kogi idan ta ba Dino tikitinta, Wike
A baya mun ji cewa Gwamna Nyesom Wike ya ce Dino Melaye bai da abun da ake bukata na zama gwamnan wata jiha.
Asali: Legit.ng