NNPP ta Kama Hanyar Shirin 2027, An Nada Wanda Zai Zama Sabon Shugaban Jam’iyya
NNPP mai alamar kwandon kayan marmari ta nada sabon shugaban rikon kwarya a Najeriya
Alhaji Abba Kawu-Ali aka zaba ya canji Farfesa Rufai Ahmed Alkali da ya sauka daga kujerar
Alkali ya tafi ne domin ya ba sababbin jini dama a Jam’iyyar NNPP da aka farfado da ita a 2023
Abuja - Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ta nada sabon shugaba na kasa wanda zai maye gurbin Rufai Ahmed Alkali.
A yammacin Alhamis, Punch ta kawo rahoto cewa Abba Kawu-Ali ya zama sabon shugaban jam’iyyar adawa ta NNPP na kasa.
Alhaji Abba Kawu-Ali zai gaji kujerar Farfesa Rufai Alkali a majalisar gudanarwa ta NWC.
Ana zaune kwatsam sai aka ji Rufai Alkali ya sauka daga kan kujerar da yake kai, ya ce akwai bukatar a samu wasu sababbin jini.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kawu-Ali ya samu karin matsayi
Gidan rediyo Najeriya ya ce kafin wannan canji da aka samu, Kawu-Ali yana cikin mataimakan shugaban jam’iyyar NNPP na kasa.
Kawu-Ali ya kasance mataimakin shugaban NNPP mai wakiltar shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, yankin da Alkali ya fito.
Kujerar ta cigaba da zama a Arewa maso gabas da ke kunshe da jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Gombe sai kuma Bauchi.
Sanarwar da aka samu a karshen makon nan ta nuna Kawu-Ali zai rike shugabancin jam’iyya na rikon kwarya, na wani lokaci.
Da wannan sauyi da aka samu, hakan yana nufin jam’iyyun PDP, LP da NNPP duk sun canza shugabaninsu bayan zaben 2023.
An rasa Farfesa Alkali
Farfesa Alkali ya taba rike mukami a majalisar NWC ta jam’iyyar PDP sannan ya zama mai ba shugaban kasa shawara a kan siyasa.
Kafin nan, tsohon shugaban na NNPP ya rike kujerar Kwamishinan ilmi da kuma na yada labarai tsakanin 2003 da 2008 a Gombe.
Dr. Babayo Liman ya bar NNPP
Daf da zabe aka samu labari wanda Rabiu Musa Kwankwaso ya dogara da shi a Arewa maso gabas, ya fice daga jam’iyyar NNPP,
Dr. Babayo Liman ya ajiye mukamin Sakataren NNPP a yankinsa da kuma jagorancin Kwankwasiyya, ya sauya-sheka zuwa PDP.
Asali: Legit.ng