Sanusi, El-Rufai, Gbaja da Jerin Sauran Mutanen da Ake Tunanin Tinubu Zai Tafi da Su

Sanusi, El-Rufai, Gbaja da Jerin Sauran Mutanen da Ake Tunanin Tinubu Zai Tafi da Su

  • Kwanaki kasa da 60 suka ragewa Asiwaju Bola Tinubu ya zama zababben shugaban Najeriya
  • Mutane duk sun zura ido domin ganin irin kamun ludayinsa, za a ga mutanen da zai ba mukamai
  • Ana kawo Muhammadu Sanusi II a cikin wadanda Tinubu zai ba mukami idan ya karbi ragama

Abuja - Wani rahoto na Leadership ya nuna cewa an fara tunanin wadanda za su samu mukamai da manyan kujeru a gwamnatin Bola Tinubu mai jiran gado.

Da aka bijiro masa da maganar a baya, zababben shugaban na Najeriya ya ce zai zakulo kwararrun mutane da suka cancanta domin ya damka masu mukamai.

Wata majiya ta shaidawa jaridar Bola Tinubu zai jawo wadanda suka taimaka masa wajen samun mukami, kuma zai tafi har da wadanda ba ‘yan jam'iyyar APC ba.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Sunayen da aka fara yawo da su a matsayin wadanda za su shiga gwamnati mai-ci sun hada da:

1. Femi Gbajabiamila

Watakila Rt. Hon Femi Gbajabiamila ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a gwamnati mai zuwa saboda irin biyayya da kusancinsa ga Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Nasir El-Rufai

Akwai masu ganin Nasir El-Rufai zai zama Sakataren gwamnatin tarayya. Gwamnan zai bar mulkin jihar Kaduna, kuma ya taba rike Ministan birnin tarayya.

3. Dele Alake

Tsakanin 1999 da 2007, Dele Alake ya rikewa Tinubu Kwamishinan yada labarai, babu mamaki ya fito cikin masu magana da yawun bakin sabon shugaban kasa.

Legit.ng Hausa ta na ganin a wannan mukami za a iya samun kwarararrun ‘yan jarida irinsu Malam Mahmud Jega, Abdulaziz Abdulaziz da Mista Bayo Onanuga.

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu a Abuja Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

4. George Akume

Lissafin da wasu su ke yi shi ne Sanata George Akume zai karbi shugabancin APC. Tsohon Gwamnan shi ne Ministan harkoki na musamman a gwamnati mai-ci.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

5. Babatunde Fashola

Babatunde Fashola shi ne magajin Bola Tinubu a Legas, bayan shekaru takwas yana Minista, za a iya ganin ya cigaba da rike wani mukamin mai tsoka a Abuja.

6. Kayode Fayemi

Ministan harkokin waje shi ne kujerar da ta fi dacewa da Kayode Fayemi a yanzu. Leadership ta ce kila zababben shugaban Najeriya zai jawo tsohon Gwamnan.

7. Dayo Adeyeye

Tun da dadewa Sanata Dayo Adeyeye yake goyon bayan tsohon Gwamnan na Legas ya zama shugaban kasa. Kamar dai Fayemi, tsohon Ministan ya fito ne daga Ekiti.

Dawowar Sanusi CBN

8. Muhammadu Sanusi II

Babu mamaki zababben Shugabanya ya kori Godwin Emefiele daga bankin CBN musamman ganin rawar da ya taka a bayan nan, ya dawo da Sanusi Lamido.

An ji labari ‘Dan sa ya yi magana, ya ce Sanusi II bai da niyyar komawa CBN, ya kuma sanar da Bola Tinubu hakan, iyakarsa da gwamnati mai zuwa ba da shawara.

Kara karanta wannan

Sirri Ya Fasu: An Gano Sunan Gwamnan Arewa da Wasu Mutum 2 da Tinubu Zai Ba Manyan Muƙamai Na Farko

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng