Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi
- Akwai wasu fitattun Gwamnoni da suka kalubalanci gwamnatin tarayya a kan batun canza manyan kudi
- Bello Matawalle ya fito fili ya na cewa matsayar da ya dauka ce ta jawo sanadiyyar rashin nasararsa
- Gwamnonin jihohin Kaduna da Kano sun garazaya kotun koli, a karshe ba su ji dadin sakamakon zabe ba
A rahoton nan, Legit.ng Hausa ta dauko Gwamnonin da suka fi zakewa wajen yin fada da gwamnati kan canjin kudin da yadda ta kaya da su a zabe.
Gwamnonin da suka yi asara
1. Abdullahi Umar Ganduje
Guguwar Rabiu Musa Kwankwaso a NNPP tayi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje illa a zaben bana, jam’iyyarsa ta rasa mulki bayan nasarar Abba Kabir Yusuf.
Baya ga zaben Gwamna, NNPP ta karbe kujerun Sanatoci biyu na Kano da ‘yan majalisar wakilan tarayya da-dama, haka lamarin yake a zaben majalisar dokoki.
Kafin zaben, Abdullahi Umar Ganduje ya caccaki Muhammadu Buhari, ya zarge shi da yunkurin kawo matsala ga jam’iyyar da ta taimakasa ya iya lashe zabe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Nasir El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen yin shari’a da gwamnatin tarayya a dalilin hana amfani da tsofaffin kudi da bankin CBN ya nemi ya yi.
A zaben 2023, PDP tayi nasara a zaben Shugaban kasa a Kaduna, sannan jam’iyyar adawar ta karbe duka Sanatoci uku da ke jihar da ‘yan majalisan wakilai goma.
Malam Uba Sani ya sha da kyar ne a zaben Gwamna da aka yi. PDP da Nasir El-Rufai ya yi wa kaca-kaca a 2019 ta samu kujerun majalisar dokoki da-dama a bana.
3. Bello Matawalle
Gwamna Bello Matawalle ya na ganin karfin sojoji aka yi amfani da su domin a hana shi zarcewa a kan kujerar Gwamnan Zamfara saboda ya yaki gwamnatin tarayya.
Dr. Dauda Lawal Dare ya doke Bello Matawalle a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum, Bungudu, Gummi, Gusau, Kaura, Maru, Shinkafi, Tsafe da Zurmi
Jam’iyyar APC ta iya samun nasara ne kurum a Bakura, Birnin Magaji, Mafara da Muradun, yankunan da Gwamna, Abdulaziz Yari da Ahmad Sani Yarima suka fito.
Jihar Kogi
Gwamna Yahaya Bello ya tsaya tsayin-daka wajen kalubalantar hana amfani da tsofaffin kudi da aka yi, hakan bai hana jam’iyyar APC galaba a jihar Kogi ba.
Sai daga baya za ayi zaben sabon Gwamna a Kogi, zuwa lokacin Muhammadu Buhari ya bar ofis.
Rikici a APC ta Delta
Rahoton da aka fitar a baya, ya nuna cewa wasu shugabannin APC na reshen jihar Delta sun kori Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin ‘dan jam’iyya mai-ci.
An zargi Ovie Omo-Agege da aikata laifuffuka da-dama da yi wa jam’iyya zagon-kasa, tare da yin aika-aikar da ta jawowa jam’iyya abin kunya a zaben bana.
Asali: Legit.ng