Ina da Ikon Naɗa Kowa Na So Har Zuwa Ranar 29 Ga Watan Mayu, Ortom
- Gwamna Ortom ya ce har zuwa ranar ƙarshe, 29 ga watan Mayu, 2023 yana da ikom naɗa duk wanda ya so
- Ya faɗi haka ne domin martani ga masu sukarsa cewa yana kokarin kulla tuggu ga gwamnati mai zuwa ta APC
- Jam'iyyar APC ta ce tana mamakin yadda Ortom ke kara naɗa wasu yayin da lokacinsa ke gab da ƙarewa
Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce yana da damar naɗa mutane a gwamnati har zuwa ranar da mulkinsa zai ƙare 29 ga watan Mayu, 2023.
Gwamnan ya bayyana haka yayin da yake martani ga nasu sukarsa kan sabbin naɗe-naɗen da ya yi a baya-bayan nan.
Ortom ya yi magana ne ta bakin Sakataren watsa labaransa, Nathaniel Ikyur, lokacin wata hira da wakilin jaridar Leadership a Ofishinsa.
Gwamna Ortom ya yi bayanin cewa yana da damar naɗa duk wanda ransa ya so a majalisar zartaswansa matuƙar ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ba ta ƙariso ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Ikyur ya ce:
"Daga yau zuwa karfe 11:00 na ranar 29 ga watan Mayu, gwamna na da cikakken ikon naɗa wanda ya ga dama, saboda haka duk masu ƙarafi kan naɗe-naɗen da aka yi yanzu sun ga zasu iya ne."
Jam'iyyar APC ta nuna rashin jin daɗinta
Idan baku manta ba jam'iyyar APC reshen jihar Benuwai, ta yi zargin gwamna Ortom na shirya wata manaƙisa ta hanyar sabbin naɗe-naɗe a lokacin da zangon mulkinsa ke gab da karewa.
A wata sanarwa, mai magana da yawun APC, Daniel Ihomun, ya ce sun samu bayanan sirri cewa Ortom ya gama shirin naɗa sabbin manyan Sakatarori da kuma ƙarin girma cikin hanzari.
Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki
A kalamansa da Punch ta rahoto, ya ce:
"Mu mambobin APC muna mamakin meyasa Ortom yake naɗe-naɗe a lokacin da zangon mulkinsa ya zo gargara maimakon ya maida hankali wajen shirin miƙa mulki."
Yadda Aka Matsamun Lamba da Makudan Kuɗi na Canja Sakamakon Zaben Gwamna, VC
A wani labarin kuma Shugabar Jami'a da ta yi aikin zaɓe a jihar Abiya ta bayyana tayin makudan kuɗin da aka mata ta yi magudi
Farfesa Oti, ta ce an mata alkawarin kuɗi masu nishi da barazanar kisa duk don ta sauya sakamakon zaɓen gwamma amma tace ba gudu ba ja da baya.
Asali: Legit.ng