Tinubu Na Bukatar Karin Addu'a Domin Ya Cimma Nasara, Gwamna Masari

Tinubu Na Bukatar Karin Addu'a Domin Ya Cimma Nasara, Gwamna Masari

  • Gwamnan Katsina ya ce shugaban kasa mai jiran gado na bukatar Addu'o'i daga bakunan 'yan Najeriya
  • Aminu Masari ya ce sun shirya taron gudanar da Addu'o'i ne ba don komai ba sai don ƙara gode wa Allah
  • Ya ce nasarar da jam'iyyar APC ta samu a jiha da ƙasa baki ɗaya duk daga Allah ne kuma mutane sun san haka

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ce zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, na buƙatar yan Najeriya su zage dantse su masa addu'a domin Allah ya dafa ma gwamnatinsa.

Masari ya faɗi haka a wurin walimar buɗe baki ta musamman da kuma Addu'o'in da aka shirya ranar Laraba a gidan gwamnatinsa da ke Katsina, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Aminu Masari.
Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari Hoto: MMC
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce shugaban kasa mai jiran gado ya saba tara Malamai da sauransu a gudanar da Addu'a kamar wannan a watan Azumin Ramadana na kowace shekara.

Kara karanta wannan

Sabbin Bayanai: Babban Tasirin da Canjin Kuɗi Ya Yi Kan 'Yan Bindiga, Masu Garkuwa da Yan Siyasa

"Wannan karon mun shirya taron ne musamman domin ƙara ƙanƙan da kai da godiya ga Allah bisa nasarar da muka samu a babban zaɓen da aka kammala kwanan nan."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba bu wani abun da zamu iya yi da ya wuce mu gode Allah mai girma da ɗaukaka bisa galabar da ya bamu a Katsina da Najeriya baki ɗaya."
"Wanna ne babban maƙasudin da ya tara mu a nan muka haɗu da Malaman Addini, Sarakunan gargajiya, jami'an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki."

- Gwamna Aminu Bello Masari.

Masari ya ƙara da cewa Allah ya riga ya baiwa Bola Tinubu shugabancin Najeriya, don haka yana bukatar addu'o'i mara iyaka don ya ba mara ɗa kunya.

"Yana kan hanyar zama sabon shugaban ƙasa, saboda haka yana buƙatar karin Addu'o'i, Alhamdulillah mun gode Allah mutane sun dawo hayyacinsu, sun gane bayan zaɓen shugabanni sai kuma subi su da Addu'a."

Kara karanta wannan

Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki

'Yadda Aka Mun Tayin Makudan Kuɗi da Barazanar Kisa Na Canja Sakamakon Zaben Gwamna'

A wani labarin kuma Shugabar jami'ar FUTO ta bayyana yadda aka mata tayin makudan kuɗi da barazana a jihar Abiya don ta sauya sakamakon zaɓe.

Farfesa Oti ta ce duk da matsin lambar da ta sha ba ta sauka daga kan dokoki da ƙa'idojin zaɓe ba, sai da ta tabbatar kuri'un al'umma sun yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262