Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni
- Gwamnan jihar Ribas ya zargi ‘Yan majalisar NWC da batar da N12.5bn da aka tara a PDP
- Nyesom Wike ya ce babu labarin duk dukiyar da jam’iyya ta samu a lokacin zaben shugabanni
- Jagoran na ‘Yan G5 ya nuna babu abin da zai hana su ganin an yi waje da Iyorchia Ayu a Jam’iyya
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zargi shugabannin jam’iyyarsa ta PDP da yin barnar makudan biliyoyin kudin da aka tara.
A yammacin Laraba, Vanguard ta rahoto Mai girma Nyesom Wike yana cewa an yi facakar abin da ya kai Naira biliyan 12.5 a watanni biyu.
Gwamnan ya jefi shugabannin PDP da wannan zargi ne yayin da yake kaddamar da wasu tituna da gwamnatinsa ta gina a yankin Obio-Akpor.
Da yake jawabi a garin Rumuigbo dazu, Wike ya na cewa jam’iyyar adawa ta PDP za ta dawo da karfinta idan aka samu canjin shugabanni.
Jawabin Nyesom Wike a Rumuigbo
Na yi amanna cewa akwai bukatar mu samu shugabanci mai karfi, ba zan goyi bayan wadanda manufarsu kurum ita ce tara kudi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba zan iya goyon bayan mutanen da mu ka yi taron jam’iyya, mu ka tara kusan N12.5bn, a cikin watanni biyu, kudin nan sun bi iska.
- Nyesom Wike
Wani ya shiga ofis na shekara daya, yanzu ya fara gina makaranta. Ba zan goyi bayan haka ba.
Ban bukatar in ba kowa hakuri. Na fada a baya, wannan ne zai kasance fada na karshe da za muyi, kuma za ayi nasara a fadan nan.
- Nyesom Wike
Bisa dukkan alamu, rahoton ya na nuna Wike bai tare da jagorancin da Iyorchia Ayu yake yi wa jam’iyyar a matakin kasa, yana so a maye gurbinsa a NWC.
"Ban ji tsoron EFCC " - Wike
A wajen ne kuma Gwamnan mai barin-gado ya sake shaidawa Duniya cewa bai tsoron hukumar EFCC, ya ce ya bi ka’ida wajen kwangilolin da ya bada.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed shi ne wanda aka gayyata domin kaddamar da wadannan ayyuka da Wike ya yi da dukiyar al’ummarsa.
Matawalle ya sallama?
Muhammad Bello Matawalle ya ce motocin sojoji 300 aka shiga da su Zamfara lokacin zabe saboda kurum a hana APC ci takarar Gwamnan 2023.
An rahoto cewa Mai girma Gwamnan Zamfara ya ce ta kai za a samu Sojoji akalla 50 a duk wata rumfar zabe, a karshe Lawal Dauda Dare ya doke APC.
Asali: Legit.ng