Sanatoci da Yan Majalisar Wakilan da Muka Ci Ba Zasu Sauya Sheƙa Ba, LP

Sanatoci da Yan Majalisar Wakilan da Muka Ci Ba Zasu Sauya Sheƙa Ba, LP

  • Ciyaman na jam'iyyar Labour Party ta ƙasa, Julius Abure, ya ce Sanatoci da 'yan majalisar wakilansu ba zasu sauya sheƙa ba
  • Ya ce a babban zaben da aka kammala, LP ta lashe kujerun Sanatoci 8 da mambobin majalisar wakilan tarayya 34
  • Shugabannin LP da zababbun 'yan majalisun sun gana a Abuja ranar Talata gabanin rantsar da majalisa ta 10

Shugaban Labour Party na ƙasa, Julius Abure, yace babu sabon zababben mamba a majalisar tarayya, wanda ya ci zaɓe karkashin inuwar jam'iyyar, da zai sauya sheka zuwa wata jam'iyya daban.

Mista Abure ya yi wannan furucin ne jim kaɗam bayan ganawa da zababbun Sanatoci da 'yan majalisar wakilan tarayya na LP ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Shugaban LP na kasa, Julius Abure.
Sanatoci da Yan Majalisar Wakilan da Muka Ci Ba Zasu Sauya Sheƙa Ba, LP Hoto: Julius Abure
Asali: Facebook

Channels tv ta rahoton shugaban LP na cewa jam'iyyarsu ta zo ta nuna banbanci ta hanyar ƙara gyarawa Demokuradiyyar kasar nan wurin zama.

Kara karanta wannan

Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki

Shugaban LP ta ƙasa ya bayyana cewa jam'iyyar ta lashe kujerun Sanatoci Takwas da mambobin majalisar wakilan tarayya 34 a zaben da aka kammala.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabinsa, Mista Abure ya ce:

"Ya zama wajibi mu yi bayani a fayyace a nan cewa duk waɗanda suka samu galaba a zaɓe karkashin jam'iyyarmu, la'alla a majalisar wakilai ko majalisar dattawa, mutanen kirki ne kuma suna nan daram a jam'iyya."
"Mutane ne da suka ƙunshi maza da mata masu gaskiya da sanin ya kamata kuma ina da tabbacin suna sane da maƙasudin da ya sa jama'a suka kaɗa musu kuri'u."
"Ko da sun gamu da matsin lamba, mambobin na da kwarin guiwar da zasu jure wannan matsi ta kowane hali."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa taron ya samu halartar manyan jiga-jigan LP na ƙasa, kuma sun maida hankali kan manufar jam'iyyar gabanin rantsar da majalisa ta 10.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Za Ta Titsiye Sanata Da Wani Dan Majalisar Wakilai Daga Jihar Gombe Bisa Zargin Cin Dunduniyar Jam'iyya

Yadda Haƙo Danyen Mai Zai Taimaki Mutanen Jihar Nasarawa - Gwamna Sule

A wani labarin kuma Gwamnan Nasarawa Ya bayyana babban amfanin hako Rijiyar man Fetur wacce Buhari ya kaddamar

Abdullahi Sule, ya ce ya ji daɗi yadda kamfanin da ke aikin ya ɗauki matasan Nasarawa aiki, zasu ƙara samun kwarewa kan abinda ya shafi albarkatun Fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262