'Yar Gwamna Mai-Ci da Jerin Duka Mata 45 da Za Su Tafi Majalisar Dokoki a Jihohi 21
- Mutane 988 za su tafi majalisar dokoki na jihohi a watan Yunin 2023, amma 48 kacal ne mata a ciki
- Hakan ya nuna mata ba su kai kashi 5% ba, duk fiye da 47% na masu kada kuri’a a kasar matan ne
- Ekiti, Kwara, Akwa Ibom su na cikin jihohin da mata suka samu kaso mai yawa a majalisar dokoki
Abuja - Wani dogon rahoto na Daily Trust ya tattaro matan da suka yi nasara a zaben majalisar dokoki da aka shirya a bana, su na jiran gado.
A jihohi 21 ne mata suka samu akalla kujera daya a majalisar dokoki, daga cikin su akwai Anambra, Kaduna, Bayelsa, Benuwai da Kuros Riba.
Sauran jihohin su ne Delta, Ekiti, Oyo, Taraba, Nasarawa, Filato, Kogi, Kwara, Akwa Ibom. Akwai Ogun, Legas, Adamawa, Ondo, Enugu da Ebonyi.
Jihohin da mata zalla ne za su kawo dokoki daga 2023 zuwa 2027 su ne: Bauchi, Borno, Gombe, Imo, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Niger, da Abia.
Kamar yadda jaridar ta kawo rahoto a ranar Lahadi, ragowar sun hada da: Osun, Rivers, Sokoto, Yobe da Zamfara, fiye da 70% duka a Arewa ne.
Anambra
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Mrs Nkechi Ogbuefi Anaocha)
Enugu
2. Hon Princess Obiajulu Ugwu (Enugu ta Kudu)
3. Hon Jane Ene (Udi ta Arewa)
Bayelsa
4. Egba Ayibanegiyefa (Yenagoa I)
5. Mrs Ebizi Ndiomu Brown (Sagbama II)
Benuwai
6. Mrs Lami Danladi (Ado)
7. Mrs Becky Orpin (Gboko ta Gabas)
Kuros Ribas
8. Rita Ayim (Ogoja)
Delta
9. Marilyn Okowa (Ika ta Arewa)
10. Bridget Anyafulu (Oshimili ta Kudu)
Ekiti
11. Mrs Bolaji Egbeyemi Olagbaju (Ado I)
12. Okuyiga Eyiyato Adeteju (Ayekire/Gbonyin)
13. Olowokere Bose Yinka (Efon)
14. Ogunlade Maria Abimbola (Emure)
15. Fakunle Okiemen Iyabo (Ilejemeje)
16. Abimbola Solanke (Moba I)
17. Maria Edeko Omozele (Esan ta Arewa maso Gabas)
Oyo
18. Olajide Olufunke Comforter (Ibadan ta Arewa)
19. Bisi Oluranti Oyewo Micheal (Ogbomosho ta Arewa)
Taraba
20. Hajiya Batulu Muhammed (Gashaka)
21. Borinica Alhassan (Bali)
Nasarawa
22. Hajara Ibrahim (Nasarawa ta Tsakiya)
Filato
23. Happiness Akawu (Pengana)
24. Salomi Tanimu (Pankshin ta Kudu)
25. Mrs Comfort Ojoma Nwuchola (Ibaji)
26. Mrs Omotayo Adeleye-Ishaya (Ijumu)
Kwara
27. Rukayat Shittu (Owode/Onire)
28. Arinola Lawal (Ilorin ta Gabas)
29. Medinat AbdulRaheem (Lanwa/Ejidongari)
30. Aishat Babatunde-Alanamu (Ilorin ta Arewa maso yamma)
31. Mariam Aladi (Ilorin ta Kudu)
Akwa Ibom
32. Selong Precious Akamba (Urua Offong Oruko)
33. Etim Itorobong Francis (Uruan)
34. Onofiok Kenim Victor (Oron/Udung Uko)
35. Ukpatu Selinah Isotuk (Ikot Abasi/Obolo ta Gabas)
36. Bolanle Lateefat Ajayi (Egbado ta Kudu)
37. Bakare Omolola Olanrewaju (Ijebu Ode)
Adamawa
38. Kate Raymond Manuno (Demsa)
39. Witherspoon Atinuke Morenike (Owo I)
40. Fayemi Olawunmi Annah (Ilaje)
41. Ogunlowo Oluwaseun (Idanre)
Ebonyi
42. Mrs Esther Agwu (Ohaukwu ta Arewa)
43. Chinyere Nwagbaga (Ebonyi ta Arewa)
Kaduna
44. Mrs Comfort Amwe (Sanga)
45. Munira Suleiman Tanimu (Lere ta Gabas)
Mata 6 sun zama 'Yan majalisa
Rahoto ya zo a baya cewa Uwargidar Gwamnan Ekiti, Olayemi Oyebanji ta ji dadin ganin sakamakon zaben ‘Yan majalisar dokoki na bana.
Uwargidar jihar ta Ekiti tayi farin cikin samun labari cewa Bose Olowookere, Bolaji Olagbaju, Abimbola Solanke da wasu mata za su je majalisa.
Asali: Legit.ng