Atiku, Peter Obi vs Tinubu: Ƙasashen Afirka 3 Inda Aka Ƙwace Nasarar Shugaban Ƙasa Bayan Zaɓe
Akalla manyan yan takara biyu ne da su ka fafata a zaben 25 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP ke kalubalantar nasarar zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da Tinubu (APC) ya samu kuri'a 8,794,726 (kaso 36.61), Atiku ya zo na biyu da kuri'a 6,984,520 (kaso 29.07). Obi yazo na uku da kuri'a 6,101,533 (kaso 25.40).
Da Atiku da Obi gaba daya sun shigar da kara kotun sauraron karrarakin zaben shugaban kasa, suna kalubalantar nasarar Tinubu.
Duka su na ikirarin su ne su ka yi nasara. Daga cikin abubuwan da suke bukata, suna neman kotun ta soke takarar Tinubu, ta ayyana su a matsayin wanda su ka lashe zaben ko soke zaben a kuma gudanar da sabon zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soke zaben shugaban kasa ya na faruwa idan kotu ko hukumar zabe ta tabbatar cewa ba a yi zaben gaskiya ba ko akwai matsaloli ko cuta a sakamakon zaben.
A wasu lokutan, za a iya soke zabe akwai shaidar aringizon kuri'a, ta'addanci, ko wasu nau'in magudin zabe. Soke zaben shugaban kasa na iya shafar siyasa, tattalin arziki, da kuma zamantakewa.
Zai iya janyo zanga-zanga, rashin daidaiton siyasa, da kuma rashin tabbas akan cigaban kasar. A wani lokacin, hakan na iya janyo rikici ko yaki.
Gaba daya, soke zaben shugaban kasa babban lamari ne da ke bukatar kulawa ta musamman don tabbatar cigaban dimukradiyya da kiyaye doka.
Atiku, Peter Obi su na da kwarin gwiwar yin nasara
Da Atiku da Obi suna da kwarin gwiwar cewa za su dawo da ''hakkinsu da aka sace'' a kotu.
Ya na da kyau, cewa, a tuna cewa tun 1999 lokacin da Najeriya ta dawo mulkin dimukradiyya, babu zaben shugaban kasar da kotu ta soke zabensa.
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Sai dai, abokan hammayar biyu za su iya samun kwarin gwiwa daga kasashen Afirka biyu da kotu ta taba kwace zaben shugaban kasa.
1. Zaben shugaban kasar Malawi na shekarar 2020
A zaben shugaban kasar Malawi na 2020, an sanar da shugaban kasa mai ci Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe zaben, amma abokin hamayyarsa Lazarus Chakwera, jagoran jam'iyyar MCP a Malawi, ya kalubalanci sakamakon a kotu.
Bayan shafe watanni ana shari'a, kotun Malawi ta soke zaben a watan Fabrairun 2020.
Kotun ta gano cewa akwai kura-kurai da yawa da kuma aringizo a wajen kirga kuri'un, ta kuma umarci a sake sabon zabe cikin kwanaki 150.
Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun farko wanda ya zama tarihi in da aka soke zaben shugaban kasa karon farko a Malawi, kuma daya a cikin kadan da ya faru a Afirka.
Yan adawa sun yi murna sosai da hukuncin, wanda ke ganin hakan a matsayin nasara ga dimukradiyya da doka.
Da Dumi-Dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Kan Soke Takarar Tinubu Da Shettima
A zaben da aka sake a watan Yunin 2020, Chakwera ya lashe zaben, in da ya kada Mutharika ya kuma zama sabon shugaban kasar Malawi. Ana kallon nasarar a matsayin wani cigaba ga dimukradiyya a kasar da kuma Afirka gaba daya.
2. Zaben shugaban kasar Kenya na 2017
Zaben shugaban kasar Kenya na 2017 ya zo da rudani, da zargin cuta, ta'addanci, da kura-kurai da su ka janyo aka sake zaben.
An gudanar da zaben ranar 8 ga watan Augusta, tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta na Jubilee da Raila Odinga a jam'iyyar NASA. An gudanar da zaben kusa da kusa, in da aka bayyana Kenyetta a matsayin wanda ya lashe da kaso 54 yayin da Odinga ke da kaso 45.
Sai dai, Odinga bai amince da sakamakon zaben ba, ya yi ikirarin an yi magudi kuma hukumar zaben kasar IEBC ta sauya alkaluman zaben saboda Kenyatta.
Jam'iyyar adawa ta shigar da kara ta na kalubalantar zaben a kotun kolin kasar Kenya.
Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu
A hukuncin da ta zartar, kotun ta soke sakamakon zaben, la'akari da kura kurai da kuma rashin bin doka wajen gudanar da zaben. Kotun ta bayar da umarnin sake zabe cikin kwanaki 60.
An sake zaben ranar 26 ga watan Oktoba, 2017, in da Kenyatta ya sa ke yin nasara, bayan da Odinga ya janye takara. Sake zaben ya gamu da rigingimu da zanga-zanga, hakan ya janyo mutuwar mutane da dama.
Zaben ya sha suka daga ma su sanya ido na kasashen waje, wanda su ka ce an yi amfani da karfin jami'an tsaro, hana yan jam'iyyar adawa zabe, da kuma rashin fayyace komai a zaben. Zaben 2017 ya bayyana irin bambancin siyasa da ke Kenya tare da fito da bukatar da ake da ita na gyara dimukradiyya a kasar.
3. Zaben shugaban kasar Ivory Cost 2010
Shi ma zaben 2010 na kasar Ivory Coast kotu ta kwace, wanda aka bayyana shugaban kasa mai ci Laurent Gbagbo a matsayin wanda ya lashe zaben, duk da yan adawa na ganin Alassane Outtara a matsayin wanda ya yi nasara. An gudanar da zaben ranar 28 ga watan Nuwambar 2010, amma ba a sanar da sakamakon ba sai da ya dauki kwanaki.
Tun da farko hukumar zabe ta bayyana Ouattara a matsayin wanda ya yi nasara, da kaso 54 na kuri'un yayin da Gbagbo ya ke da kaso 46. Sai dai, kotun zabe, wanda ke da alhakin karshe kan sakamakon, ta yi watsi da sakamakon, ta ce akwai kurakurai a wasu sassa ta kuma bayyana Gbagbo a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso 51 na kuri'u.
Bayyana sabon sakamakon zaben ya janyo rikicin siyasa da tashin hankali a Ivory Coast, yayin da Gbagbo da Ouattara kowa ke ikirarin shi ne shugaban kasa kuma kafa adawa mai karfi.
Rikicin ya janyo yaki, yayin da jami'an tsaro ma su goyon bayan Ouattara su ka kwace mulkin kasar a watan Afrilu 2011 da taimakon jami'an Faransa da na majalisar dinkin duniya.
An kama Gbagbo da gurfanar da shi a kotun sauraron manya laifuka ta duniya Hague, in da aka tuhume shi da laifukan cin zarafin dan adam. An nada Ouattara a matsayin shugaban kasa kuma ya dinga lashe zabe a sauran zabukan da su ka dinga gudana a kasar.
Obi ya hadu da Olusegun Obasanjo a filin tashin jiragen sama na Anambra
A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ya hadu da Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya a garin Awka, babban birnin jihar Anambra.
Kamar yadda Obi ya wallafa a shafinsa na Twitter wanda Legit.ng ta gani a ranar Lahadi, ya yi farin cikin samun damar tattaunawa da tsohon shugaban kasar.
Asali: Legit.ng