Yadda Aka Min Tayin N100m Don In Janye Takara, Dan Shekaru 33 Da Ya Kayar Da Kakakin Majalisar Yobe

Yadda Aka Min Tayin N100m Don In Janye Takara, Dan Shekaru 33 Da Ya Kayar Da Kakakin Majalisar Yobe

  • Matashi dan shekara 33, Lawan Musa Majakura, ya bada labarin yadda aka masa tayin N100m don ya janye takararsa
  • Majakura, zababben dan majalisa a jihar Yobe ya ce sau biyu wasu mutane da ya yi imanin suna wakiltar Ahmed Mirwa, kakakin majalisar Yobe suka masa tayin kudi
  • Zababben dan majalisar ya ce ya ki amincewa da kudin bayan ya yi shawara da mutanensa, ya kuma ce wannan ba shine takararsa na farko ba a siyasa

Lawan Musa Majakura, dan shekara 33 da ya kayar da kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Ahmed Mirwa a zaben ranar 18 ga watan Maris, ya bayyana yadda aka masa tayin Naira miliyan 100 don ya janye takararsa.

Da ya ke magana a hirar da Daily Trust ta yi da shi, zababben dan majalisar karkashin jam'iyyar PDP, ya ce ya yi nasarar lashe zaben ne saboda gagarumin gudunmawa da ya samu daga mutanen yankinsa duk da cewa shi ba mai hannu da shuni bane.

Kara karanta wannan

"Yadda Shugaban Majalisar Da Na Kayar Ya Sa Aka Kama Ni Lokacin Azumin Ramadan", Matashin Da Ya Ci Zabe a Yobe

Lawan
An bani N100m don in janye takara amma na ki yarda, Dan shekara 33 da ya kayar da kakakin majalisar Yobe. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ya ce:

"Lokacin kamfen din mu, mun fuskanci tsoratarwa da cin mutunci daga wasu saboda banbancin siyasa, amma, mun gode wa Allah duk da kallubalen, mun yi nasarar cin zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba abu mai sauki bane kallubalantar Kakakin Majalisar Dokokin Jiha.
"Maganar gaskiya, shi (kakakin majalisar) bai tuntube ni da kansa don in janye masa ba amma wani jami'in gwamnati da kuma wasu mutane da na ke ganin wakilansa ne sun zo wuri na har sau biyu, suna cewa in janye. Sunyi alkawarin bani naira miliyan 18, amma na ki. Daga bisani, sun dawo sun min tayin naira miliyan 100, amma ban yarda ba. Na ma fada wa mutane ne abin da muka tattauna amma dukkan mu mun yarda cewa ba zan janye ba, sai muka cigaba da kamfen din mu."

Ya kuma bayyana cewa wannan nasarar tasa ba shine karon farko da ya fara shiga takarar siyasa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Ya ce:

"Eh, na taba takarar kujerar kansila a 2021 lokacin ina jam'iyyar APC kafin in shiga PDP, amma ba samu tikiti ba. Mutanen mu, musamman matasa, sun ce in yi takara saboda suna ganin zan yi abin da ya fi baya. Amma Allah bai bamu ba. Don haka muka yi addu'a ya bamu wanda ya fi alheri."

Takaitaccen tarihin karatun zababben dan majalisar na Yobe

Ina da difiloma a bangaren Public Administration da Management daga Atiku Abubakar Collage of Legal and Islamic Studies, Nguru, a 2013.

Bayan haka, na tafi Federal Polytechnic, Damaturu don yin National Diploma da Higher National Diploma a Business Administration a 2020.

Ban yi NYSC ba

Shekaru na sun haura 30 lokacin da na gama HND don haka aka bani satifiket din yafe yin NYSC. Ina sayar da kifi da wasu sana'o'in da za su bani taro da kwabo. Ina da mata da yaya hudu.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

Matashi Ya Kayar Da Kakakin Majalisa Wanda Ya Yi Fiye Da Shekaru 20 Kan Kujerar Wakilci a Majalisar Yobe

Tunda farko, kun ji cewa Honarabul Ahmed Mirwa Lawan ya sha kaye a hannun matashi Lawan Musa na jam'iyyar PDP, mai wakiltar Nguru II.

Dakta Habib Muhammad, baturen zabe na jihar Yobe ya sanar da cewa Musa ya samu kuri'u 6,648, inda ya yi nasara kan Lawan na APC wanda ya samu kuri'u 6,466.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164