"Yadda Kakakin Majalisar Da Na Kayar Ya Sa Aka Kama Ni a Lokacin Ramadan" – Zababben Dan Majalisar Yobe

"Yadda Kakakin Majalisar Da Na Kayar Ya Sa Aka Kama Ni a Lokacin Ramadan" – Zababben Dan Majalisar Yobe

  • Zababben dan majalisar jihar Yobe, Lawan Musa Majakura, ya magantu kan yadda aka kwamushe shi sau biyu saboda sukar yan siyasa
  • Matashin wanda ya kayar da shugaban majalisar Yobe ya ce Ahmed Mirwa Lawan ya sa an kama shi saboda ya soke shi kan rashin shugabanci mai kyau
  • Majakura dai ya kafa tarihi a zaben 2023 inda ya kayar da kakakin majalisar dokokin jihar Yobe wanda ya nemi komawa majalisar a karo na 6

Yobe - Zababben dan majalisa mai shekaru 34, Lawan Musa Majakura ya yi bayanin yadda kakakin majalisar dokokin jihar Yobe da ya kayar, Ahmed Mirwa Lawan, ya sa aka kama shi bayan ya soke shi kan rashin wakilci mai kyau.

Majakura ya kayar da kakakin majalisar kuma dan majalisa mai wakiltan mazabar Nguru 11 da ke karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe a zaben da aka yi da kuri'u 182.

Kara karanta wannan

Dani za a yi: Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa

Kakakin majalisar Yobe da zababben dan majalisa
Yadda Kakakin Majalisar Da Na Kayar Ya Sa Aka Kama Ni a Lokacin Ramadan – Zababben Dan Majalisar Yobe Hoto: Lawan Musa
Asali: Twitter

Zababben dan majalisar wanda ya yi takara karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya fada ma jaridar Daily Trust yadda aka kama shi sau biyu a wata hira ta wayar tarho.

Sau biyu yan siyasa na sa a kama ni saboda ina sukar su, zababben dan majalisa

Jaridar ta nakalto lawan yana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A zahiri, an kama ni sau biyu. Daya daga cikinsu ya kasance daga wani dan siyasa a jam'iyyar APC kafin na bar jam'iyyar, bayan na soke shi a Facebook. Ya fada ma yan sandan cewa su kama ni sannan su tsare ni na kwanaki biyar.
"Na biyun ya kasance daga kakakin majalisa, wanda na kayar. Na soke shi a kan rashin wakilci mai kyau sannan aka kama ni aka kuma tsare ni na awanni 48. A shekarar bara ne lokacin Ramadan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

"Sun kama ni saboda na tsaya tsayin daka da mutanena. Misali, a duk sanda na ji cewa gwamnatin jiha ta amincewa yan majalisa da wani aiki na wata mazaba, na kan tabbatar da a ina ne aka aiwatar da namu da kuma ko ya amfani al'ummarmu? Wadannan na daga cikin tambayoyin da na kan yi wa kaina. Harma na kan bi su don tabbatar da an yi aikin. Don haka na kan soke shi a duk sanda na gano cewa muna da matsalar da zai iya magancewa amma ya ki yin hakan. Kuma zan soke shi ne da hujjoji."

Dan shekaru 35 ya raba kakakin majalisar Yobe da kujerarsa

Mun dai kawo a baya cewa Ahmed Mirwa Lawan, shugaban majalisar Yobe ya sha kaye a hannun Lawan Musa, dan takarar jam'iyyar PDP, mai shekara 35 a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel