Dan Takarar Gwamnan Jam'iyyar PRP, Ya Taya Uba Sani Murnar Cin Zaben Gwamnan Kaduna

Dan Takarar Gwamnan Jam'iyyar PRP, Ya Taya Uba Sani Murnar Cin Zaben Gwamnan Kaduna

  • Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a jihar Kaduna ya amince da ƙaddarar kayen da ya sha zaɓen
  • Hayatudden Lawal Makarfi bai yi ƙasa a guiwa ba inda ya zaɓaɓɓen gwamnan jihar nasarar da ya samu a zaɓen
  • Zaɓaɓɓen gwamnan ya nuna jinɗaɗin sa dangane da hakan inda ya gayawa masa cewa ƙofarsa a buɗe take ga duk mai son cigaban jihar

Jihar Kaduna- Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Hayatudden Lawal Makarfi, ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar murnar nasarar da yayi a zaɓe.

Hayatudden ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna Mallam Uba Sani, murnat lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris 2023. Rahoton The Cable

Kaduna
Dan Takarar Gwamnan Jam'iyyar PRP, Ya Taya Uba Sani Murnar Cin Zaben Gwamnan Kaduna Hoto: The Cable
Asali: UGC

Uba Sani, wanda yayi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu ƙuri'u 730,002 inda yayi nasara kan mai bi masa a zaɓen Isa Ashiru na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya samu ƙuri'u 719,196.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 12 da INEC ta taimakawa Tinubu yaci zabe, Atiku

Zaɓaɓɓen gwamnan shine ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PRP, a yayin wata ziyar taya murna da ya kai gidan zaɓaɓɓen gwamnan ranar Alhamis, yayi masa addu'ar samun damar gudanar da mulki wanda zai amfani al'ummar jihar ta Kaduna.

Uba Sani, a na shi jawabin ya bayyana cewa ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PRP, ya nuna halin dattako inda ya nuna godiyar sa kan wannan ziyarar da ya kawo masa.

Zaɓaɓɓen gwamna ya kuma tabbatarwa da ɗan takarar na PRP cewa ƙofar sa a buɗe take ga duk wanda yake son kawo gudunmawa dangane da cigaban jihar.

Dan Takaran Gwamnan Kaduna Zai Kai Jam’iyyar PDP Kotu Duk da Ya Ci Zabe

A wani labarin na daban kuma, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna yace zai maka jam'iyyar adawa ta PDP a kotu duk da ya ci zaɓe.

Uba Sani ya samu nasara akan ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel