Tinubu: Minista Ya Rubutawa DSS Wasika, Ya Nemi a Cafke Peter Obi da Baba Ahmed

Tinubu: Minista Ya Rubutawa DSS Wasika, Ya Nemi a Cafke Peter Obi da Baba Ahmed

  • Festus Keyamo SAN ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban hukumar DSS, kuma an karbi takardar
  • Ministan kwadago da samar da ayyukan kasar yana karar Peter Obi da Dr. Datti Baba-Ahmed
  • Keyamo ya ankarar da jami’an tsaro kalaman da ‘yan takaran LP ke yi za sui ya tada zaune tsaye

Abuja - Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na tarayya, Festus Keyamo ya kai korafin Peter Obi da Datti Baba-Ahmed wajen DSS.

Festus Keyamo SAN ya yi magana a shafin Twitter a ranar Alhamis, ya ce shi da kan shi ya rubuta takarda, yana kai korafin ‘yan takaran gaban hukuma.

Ministan ya dauki wannan mataki yana mai neman jami’an tsaro su cafke ‘dan takaran shugaban kasar da abokin gaminsa saboda kalaman su.

Keyamo yake cewa abin da Peter Obi da Yusuf Datti Baba-Ahmed suke fada game da zaben shugaban Najeriya zai iya kawo karshen damukaradiyya.

Kara karanta wannan

Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

Abin ya fara yawa - Minista

Premium Times ta bi labarin, ta rahoto Ministan yana zargin wadannan mutane biyu da yin abubuwan da za su iya harzuka jama’a a kan gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A takardar korafin da Keyamo SAN ya rubuta, ya ce Obi da Datti sun fara wuce gona da iri.

Festus Keyamo
Festus Keyamo SAN Hoto: sunnewsonline.com
Asali: Twitter

Rahoton ya ce Lauyan ya kafa hujja da wata hira da aka yi da Dr. Datti Baba-Ahmed, inda aka ji ta kai yana yi wa tsarin farar hular Najeriya barazana.

Wadannan kalamai da ikirari sun tsallake iyakar ‘yan kasa na hakkin magana da kuma nuna rashin jin dadinsu a fili, su na kiran a rusa damukaradiyya.
Sun dage a bi wasu hanyoyi da tsarin mulki bai san da su ba. A wasu wurare, ta kai su na amfani da bakin wasu, su na kiran a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Sanatan Jihar Kano Ya Shiga Sahun Masu Neman Kujerar Majalisar Dattawa a 2023

- Festus Keyamo SAN

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta fahimta, wannan takarda ta shiga ofishin Darekta Janar na DSS da ke Abuja, an kuma sa hannu a ranar 23 ga watan Maris.

Da yake magana a shafinsa, Keyamo ya ce zai yi magana a gidan talabijin domin fayyace zargin da ake yi, kafin nan ya nuna neman zaman lafiya shi ya fi.

Peter Obi ya tafi kotu

A yau aka samu rahoto cewa Peter Obi ya gabatar da ikirarin da ke nuna akwai Jihohin da Hukumar INEC ta taya Bola Tinubu yin magudi a zaben bana.

LP ta ce mutane 205,110 da 329,003 suka zabe ta a Ribas da Benuwai, amma aka ce APC ta ci zabe, don haka ta bukaci a sake shirya zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng