Bayan Shan Kaye Hannun APC, Ortom Ya Kafa Kwamitin Mika Mulki A Ranar 29 Ga Watan Mayu

Bayan Shan Kaye Hannun APC, Ortom Ya Kafa Kwamitin Mika Mulki A Ranar 29 Ga Watan Mayu

  • Gwamnan jihar Benue ya fara shirye-shiryen mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • A ranar Laraba, 22 ga watan Maris, Ortom ya kafa kwamitin mika mulki da zai kula da mika mulkin ga sabuwar gwamnatin jihar ta All Progressives Congress, APC
  • A bangare guda, Rabaran Fada Hyacinth Alia, zababben gwamnan jihar na Benue ana fatan zai kama aiki ne a ranar 29 a watan Mayun 2023, kuma zai mulki jihar na tsawon shekaru hudu

Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a ranar Laraba, 22 ga watan Maris, ya kafa kwamitin da zai shirya mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Gwamnan wanda ya jagoranci taron majalisar zartarwa na jihar da aka yi a ranar Laraba a gidan gwamnatin Benue a Makurdi ya sanar da kafa kwamitin, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu

Gwamna Ortom
Ortom ya kafa kwamitin bikin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Hoto: Gwamnatin Jihar Benue
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin kwamitin na mika mulki

Ortom ya sanar da cewa Farfesa Tony Ijohor SAN, sakataren gwamnatin jihar Benue ne zai zama shugaban kwamitin tare da yan majalisar zartarwa na jihar a matsayin mambobi.

Direkta na EXCO, Bartholomew Aondoaver Ageraga, shine zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

Gwamnan ya ce ana fatan kwamitin zai kammala rahotonsa cikin sati uku.

Zaben gwamnan Benue na 2023: Dalilai uku da suka sa Rabaran Alia ya yi nasara

A ranar Litinin 21 ga watan Maris, Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana Rabaran Fada Hyacinth Alia na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin zababben gwamnan jihar Benue.

Alia ya yi nasara bayan samun kuri'u 473,933 yayin da abokin fafatawarsa Titus Uba na PDP ya samu kuri'u 223,913.

Amma wasu dalilai uku ne suka yi sanadin nasararsa kamar haka.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Borno

Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom Ya Sha Kaye Zaben Sanata, Dan Takarar APC Ya Lashe Zaben

Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya gamu da rashin nasara a zaben sanata na mazabar Benue North West da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu inda dan takarar APC, Cif Titus Zam ya ci zaben.

Ortom ya samu kuri'u 106,882 yayin da dan takarar na APC, Zam ya samu kuri'u mafi rinjaye na 143,151, sai shi kuma dan takarar jam'iyyar Labour, Mark Gbillah ya samu kuri'u 51,950 kamar yadda The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel