Gwamna Ya Taya Tinubu Murna Bayan Kwana 21, Ya Nemi Bukata 1 a Gwamnatinsa
- Gwamnan Jihar Anambra ya fitar da jawabi, yana taya Asiwaju Bola Tinubu murnar nasara
- Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya ce tun da an lashe zabe, sai a maida hankali kan mulki
- Gwamna Soludo ya bada shawarar a fito da Nnamdi Kanu domin Ibo su iya samun zaman lafiya
Anambra - Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya aika sakon taya murna ga Asiwaju Bola Tinubu a kan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa.
This Day ta rahoto Charles Chukwuma Soludo ya aika sakon barka ga zababben shugaban Najeriyan da sauran wadanda suka yi nasara a zaben bana.
Mai girma Gwamnan ya fitar da jawabi da hannunsa a ranar Talata, yana mai yabawa matasan Najeriya, ya ce su ne asalin gwarazan zaben 2023.
"Bari in yi amfani da wannan dama domin taya murna ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a kan wannan zaben.
Mu na taya sauran abokan hamayyarka murna da irin jarunta da kokarin da suka yi a takarar.
Najeriya ta na bukatar dinke baraka, sauyin fasalin kasa da kuma magance manyan matsaloli na rashin tsaro da kuma tattalin arziki."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Charles Chukwuma Soludo
Siyasa ta wuce
Ganin zabe ya kare, Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya ce ya kamata a maida hankali wajen magance matsalolin da ke damun Najeriya.
Gwamnan na APGA yake cewa matsalar tsaron da ta addabi Kudu maso gabas abin a duba ne. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a safiyar Talata.
Farfesa Soludo ya ce yadda za a shawo kan lamarin yankin Ibo shi ne a fito da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu wanda ya dade a garkame.
Tsohon Gwamnan na babban bankin Najeriya yana nan a kan bakarsa, yana ganin cewa sakin Nnamdi Kanu zai taimaka wajen kawo zaman lafiya.
Ibo ya zama 'Dan majalisa a Sardauna
A baya an samu labari wani Mai ba Gwamnan jihar Taraba shawara, Nelson Len wanda Inyamuri ne asalin shi, zai tafi Majalisar dokoki a 2023.
A majalisar dokokin Taraba, PDP ta na da rinjaye da 58%, NNPP, APC da SDP su na da kujeru goma. Daga cikin zababbun 'yan majalisa akwai mata.
Asali: Legit.ng