Sakamakon Zaben Gwamnonin 2023: Kebbi, Abia Da Sauran Jihohin Da Ba a Sanar Da Wadanda Suka Lashe Zabe Ba

Sakamakon Zaben Gwamnonin 2023: Kebbi, Abia Da Sauran Jihohin Da Ba a Sanar Da Wadanda Suka Lashe Zabe Ba

Zaben gwamnonin Najeriya na 2023 na ta zuwa karshe a hankali yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana wadanda suka lashe zabe a fadin jihohi 28.

Zuwa yanzu, hukumar zaben ta sanar da wadanda suka lashe zabe a jihohi 24 cikin 28 da aka gudanar da zaben gwamnonin.

Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
Sakamakon Zaben Gwamnonin 2023: Kebbi, Abia Da Sauran Jihohin Da Ba a Sanar Da Wadanda Suka Lashe Zabe Ba
Asali: Original

Har yanzu ba a sanar da wadanda suka lashe zabuka a sauran jihohi hudu ba saboda wasu dalilai.

Jihohin da ake magana a kansu sune:

  1. Jihar Adamawa
  2. Jihar Enugu
  3. Jihar Kebbi
  4. Jihar Abia

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jihar Abia: An dakatar da tattara sakamako

A ranar Litinin, 20 ga watan Maris, jami'in zabe na jihar, Farfesa Nnenna, ta sanar da dakatar da shirin tattara sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Farfesa Nnenna ta ce INEC ta bayar da umurnin dakatar da tattara sakamako daga karamar hukumar Obingwata jihar bayan yan daba sun farmaki ofishin hukumar zaben da ke yankin karamar hukumar.

Jihar Enugu: An dakatar da tattara sakamako

INEC ta kuma bayar da umurnin dakatar da shirin tattara sakamakon zabe a jihar Enugu. Hukumar ta ce za ta yi nazarin sakamako daga kananan hukumomi biyu.

Kananan hukumomin da abun ya shafa sune Nsukka da Nkanu ta gabas.

Jihohin Adamawa da Kebbi states: An ayyana zabukan a matsayin ba kammalallu ba

Ba a riga an samu wadanda suka lashe zabe ba a zaben gwamnonin Adamawa da Kebbi ba saboda an ayyana zabukan a matsayin ba kammalallu ba.

A Adamawa, INEC ta ayyana zaben a matsayin ba kammalalle ba saboda tazarar da ke zaben.

Yar takarar jam'iyyar APC a jihar, Sanata Aishatu Dahiru Binani ta samu kuri'u 390, 275, in da gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri, na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 421,524.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An sace ma'aikatan INEC 2 dauke da sakamakon zaben gwamnan wata jihar Arewa

Koda dai sakamakon zaben karshe da INEC ta hada ya nuna cewa Gwamna Fintiri ne ya samu mafi yawan kuri'u, INEC ta ce yawan kuri'un da aka soke ya fi tazarar da ke tsakanin dan takarar PDP da Binani.

An sanya ranar sake zabe a yankunan da ba a yi zabe ba a jihar.

A jihar Kebbi, an ayyana zaben a matsayin ba kammallale ba saboda kuri'un sun zarta.

Yusuf Sa'idu, baturen zaben ya ce an ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba saboda an soke kuri'u masu yawa kuma an samu wanda suka zarta a kananan hukumomi 20 cikin 21 na jihar.

Sa’idu ya ce jimilar masu rijista ita ce 2,032,041 wanda a ciki jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri'u 388,258 sannan Peoples Democratic Party (PDP) ta samu 342,980, inda aka samu banbancin kuri'u 45,278.

Gwamnatin Zamfara ta saka dokar kulle a fadin jihar

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita a fadin jihar bayan sanar da wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng