Dan Takarar Gwamnan Jihar Oyo Na APC Ya Rungumi Kaddara Ya Taya Abokin Karawar Sa Murna
- Ɗan takarar gwamnan All Progressives Congress (APC) a jihar Oyo, ya amince da shan kashin da yayi a zaɓen
- Teslim Folarin na jam'iyyar APC ya taya takwaran sa na jam'iyyar PDP, gwamna Seyi Makinde murnar sake lashe zaɓen sa da yayi
- Ɗan takarar ya kuma aike da saƙon godiyar sa ga al'ummar jihar bisa goyon bayan da suka ba shi
Jihar Oyo- Ɗan takarar gwamnan jihar Oyo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progessives Congress (APC), Tesl Folarin, ya taya gwamnan jihar murnar lashe zaɓen da yayi.
Teslim Folarin ya aike da sakon taya murnar ne ga gwamnan kuma ɗan takarar na jam'iyyar PDP, Seyi Makinde, a ranar Litinin a zaɓen da aka kammala na ranar Asabar. Rahoton Punch
Gwamna Makinde ya samu ƙuri'u 563,756, inda ya samu nasara kan Teslim Folarin na jam'iyyar APC wanda ya su ƙuri'u 256,685, yayin da Adebayo Adelabu na jam'iyyar Accord Party ya samu ƙuri'u 38,357. Rahoton Inside Oyo
A wata sanarwa da Folarin ya rattaɓawa hannu da kan sa ranar Litinin, ya bayyana cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Bisa bayyana sakamakom zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) tayi a hukumance, ina taya Seyi Makinde Murna."
"Ina kuma miƙa saƙon godiya ta ga mutanen jihar Oyo, bosa goyon bayan da suka ba ƴan takarar jam'iyyar APC a zaɓukan ranar 25 ga watan Fabrairu da ranar 18 ga watan Maris. Allah yayi muku albarka."
“Ga duk wanda aka ɗorawa nauyi, akwai ƙalubale a kansa. A dalilin haka ne nake ɗumbin godiya ta shugabanni da mambobin jam'iyyar mu ta APC, da dukkanin waɗanda suka mara mana baya daga wasu jam'iyyun."
“Haka kuma ina miƙa saƙon godiya ta ga mambobin kwamitin kamfen na APC na zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na jihar Oyo. Nagode muku bisa biyayyar ku, jajircewar ku da kuma riƙe alƙawarin ku kan abinda muka sa a gaba."
Sa’o’i Kadan da Kammala Zabe, Sanata Ya Fice Daga PDP, Ya Rungumi Tinubu da Kyau
A wani rahoton kuma, kun ji cewa ɗan takarar sanatan PDP ya fice daga jam'iyyar bayan ya sha kashi a zaɓen sanata.
Chimaroke Nnamani ya sha kashi ne a zaɓen sanatan Enugu ta Gabas.
Asali: Legit.ng