APC Ta San Makomar ta, An Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna a Nasarawa
- Abdullahi A. Sule ya yi nasara a zaben Gwamnan Jihar Nasarawa da aka shirya a makon jiya
- Gwamnan zai cigaba da mulki zuwa watan Mayun 2023 bayan ya yi galaba a kan Jam’iyyar PDP
- Burin David Ombugadu na zama Gwamna bai tabbata, PDP ta nuna za ta shigar da kara a kotu
Nasarawa - A ranar Litinin, 20 ga watan Maris 2023, hukumar INEC ta tabbatar da cewa Gwamna Abdullahi A. Sule zai zarce a kan kujerarsa.
Rahoton tashar talabijin na Channels ya tabbatar da cewa Mai girma Abdullahi A. Sule ya yi nasara a jam’iyyar APC a zaben Gwamna da aka yi.
Baturen zaben Gwamna a Nasarawa, Farfesa Tanko Ishaya ya ayyana jam’iyyar APC a matsayin wanda ta lashe zaben bana da kuri’u 347, 209.
Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne David Ombugadu na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 283,016.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kotu za ta raba gardama
Rahoton ya ce amma jam’iyyar hamayya ta PDP ta nuna ba ta ji dadin sakamakon da aka sanar ba, ta shaida cewa za ta shigar da kara a kotun zabe.
Haka zalika APC da tayi nasara a zaben na ranar Asabar, ta ce za ta shigar da kara a kotu, ta kalubalanci nasarar da PDP ta samu a wasu wurare.
Sule ya gagari 'Yan adawa
The Guardian ta ce a zaben 2019, David Ombugadu ya gwabza da A. A Sule, amma bai kai labari ba. A wancan lokci PDP ta samu kuri’u 184, 281 ne.
Wannan karo ‘dan takaran PDP ya hada kai da tsohon Minista, Labaran Maku wanda yake neman mulki a APGA domin a kifar da gwamnatin APC.
Sau biyu a jere kenan Injiniya Sule yana Ombugadu a zaben Gwamna a jihar Nasarawa.
Zaben Jihar Legas
An samu labari mutane 1,182,620 aka tantance a zaben, a ciki kusan 65% sun zabi Jam'iyyar APC, Gwamna Babajide Sanwo Olu zai zarce a mulki.
Gbadebo Rhodes-Vivour ya yi nasara a karamar hukuma daya ne rak, yana da kuri'u 312,329 sai kuma 'dan takaran jam'iyyar PDP ya ci kuri'u 64, 000.
Asali: Legit.ng