Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Kulle Daga Safe Har Dare

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Kulle Daga Safe Har Dare

  • Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta jihar Kano ta saka dokar hana fita na daga safe har dare a fadin jihar
  • An dauki wannan matakin ne domin hana barkewar rikici a jihar wacce ta dauki dumi sakamakon zaben gwamna
  • Kwamishinan labaran jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ne ya fitar da sanarwar inda ya bukaci jama'a su zauna a gida

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta saka dokar kulle na daga safe har dare, a kokarinta na hana barkewar rikici sakamakon halin fargabar da ake ciki a jihar.

Jama'a dai sun shiga halin dar-dar a jihar sakamakon tattara sakamakon zaben gwamna da na yan majalisar jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje yana jawabi
Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Kulle Daga Safe Har Dare Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba, ya fitar a safiyar Litinin, 20 ga watan Maris, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'in Tattara Sakamakon Zabe A Kano Ya Yanke Jiki Ya Fade A Hedkwatar INEC

Ya ce an yanke shawarar sanya dokar ne domin hana yan daba haddasa rikici a jihar wacce ta rigada ta dauki dumi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da kasancewa a cikin gidajensu kasancewar jami'an tsaro ba za su kyale duk wanda suka samu ko kungiyar da ta yi kokarin ta da zaune tsaye ba.

INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano

A halin da ake ciki, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano na shekarar 2023.

Baturen zabe na jihar, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim, ya bayyana cewa Yusuf ya samu kuri'u 1,019,602 yayin da dan takarar APC, Nasir Yusuf Gawuna ya samu kuri'u 890,705.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Kwankwaso Da Buba Galadima Sun Dira Ofishin INEC A Kano Yayin Da Ake Jiran Sakamako Zabe

A baya mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya dira ofishin hukumar zabe ta kasa a jihar Kano.

Kwankwaso ya yi wa ofishin tsinke ne tare da Buba Galadima yayin da ake jiran tsammani kafin sanar da sakamakon wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a jihar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel