2023: Yadda Ta Kaya da Manyan Masu Neman Takara a Akwatinsu a Zaben Jihohi
- Abuja - Yayin da sakamakon zaben Gwamnonin jihohi da majalisar dokoki suke fitowa a fadin Najeriya, an bi rumfuna wasu daga cikin ‘yan takaran.
- Daily Trust ta tattaro bayanai a kan sakamakon yadda zabe ya kasance a wasu akwatin da masu neman takara suka kada kuri’arsu a zaben ranar Asabar.
1. APC ta kunyata
Rumfar Gbadebo Rhodes-Vivour da ke Anifowoshe a Ikeja ta fada hannun Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu da kuri’u 18 da 29, PDP ta samu 3 kacal.
2. Mataimakin Gwamnan Bauchi
Sadique Abubakar ya yi nasara a akwatin Baba Tela wanda shi ne Mataimakin Gwamna Bala Mohammed a Bauchi, APC ta samu 165, PDP ta na da 113.
3. Makinde ya gagari Folarin
‘Dan takaran jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Oyo, Teslim Folarin bai iya kawo akwatinsa a Idi Ose da ke Ona Ara ba, PDP ta doke shi da kuri’u 196 da 89.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
4. …Gwamna ya yi nasara
Jaridar ta ce Gwamna Seyi Makinde da ya yi zabe a garin Ibadan ya tashi da kuri’u 174 a akwatinsa, jam’iyyar APC mai adawa ta tsira da 28 ne rumfar gwamna.
5. Ortom ya rasa gidan Gwamnati
A Benuwai, Rabaren Hyacinth Alia ne ya yi galaba a duka akwatun zaben da ke cikin gidan Gwamnati. Kafin yanzu rahotanni sun tabbatar da wannan.
A wani akwatin APC ta samu kuri’u 130, PDP kuwa ta na da 43. A akwatunan da ke fadar gwamnati, Titus Uba ya samu 10, ‘dan takaran APC ya ci 36.
6. Sir Kashim Ibrahim House
Haka abin da yake a gidan Gwamnatin jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya samu kuri’u 77 da 69 a akwatuna biyu na gidan gwamnati, Uba Sani ya ci 40 da 64.
7. Zaben Gwamnan Kano
Legit.ng Hausa ta fahimci Nasiru Yusuf Gawuna ya lallasa NNPP a mazabar Gawuna a Nasarawa, Abba Kabir Yusuf ya kawo akwatinsa da yake cikin Gwale.
8. Ubandoma a Sokoto
A akwatinsa, Saidu Ubandoma mai takarar Gwamna a jihar Sokoto ya tashi da kuri’u 427, ya doke Ahmad Aliyu da ya tsaya a jam’iyyar APC, yana da kuri’u 4.
'Ku karbi kudinsu' - Buhari
A jiya aka samu labari Shugaban Najeriya ya kada kuri’arsa a agarin Daura, wannan ne zabensa na karshe yana kan kujerar shugaban kasa a Najeriya.
APC tayi nasara a rumfar, kuma Muhammadu Buhari ya yi babban kira ga jama'a da ‘yan siyasar da suke amfani da kudinsu wajen sayen kuri’u a zabe.
Asali: Legit.ng