Tinubu Ya Magantu Kan Gwamnatin Da Zai Kafa, Ya Yi Watsi Da Batun Gwamnatin Hadin Gwiwa

Tinubu Ya Magantu Kan Gwamnatin Da Zai Kafa, Ya Yi Watsi Da Batun Gwamnatin Hadin Gwiwa

  • Asiwaju Bola Tinubu, zababben shugaban kasar Najeriya ya kore yiwuwar kafa gwamnatin hadin gwiwa
  • Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce zai kafa gwamnatinsa ne bisa cancanta da iya aiki da halaye masu kyau ba kabila ko addini ba
  • Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya, wadanda suka goyi bayansa da ma wadanda ba su zabe shi ba su bashi hadin kai don gina kasa

Zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, ya kore batun kafa gwamnatin hadin gwiwa, yana mai cewa manufofi na sun dara hakan.

Zababben shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar da kansa a ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto.

Tinubu, wanda ya bayyana kansa a matsayin bawa, ya ce shi da tawagarsa suna tattaunawa tare da kaifafa hanyoyin da gwamnatinsa za ta magance matsalolin kasar kuma za su fara aiki da ya shiga ofis.

Kara karanta wannan

Toh fa: Buhari ya ce yana son Tinubu ya ci gaba da yiwa 'yan kasa abu 1 da yake yi

Bola Tinubu
Tinubu Ya Magantu Kan Gwamnatinsa, Ya Yi Watsi Da Gwamnatin Hadin Gwiwa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wani sashi cikin jawabinsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A matsayin shugaban kasa mai jiran gado, na yi na'am da aikin da ke gaba na. Ana maganan gwamnatin hadin gwiwa. Gwamnatin kasa na cancanta na ke so. Wurin zaben gwamnati na, ba zan bada muhimmanci kan wasu abu da ba kwarewa da cancanta ba. Lokacin yin siyasa ya wuce.
"Zan tattaro maza da mata da matasa wadanda suka cancanta daga dukkan sassan Najeriya. Matan za su kasance fitattu. Ko addinin ka yasa kana zuwa coci ko masallaci ba zai yi tasiri wurin samun mukami a gwamnati ba. Cacanta da hali mai kyau za a duba.
"Tsare kasarmu da nasararsa ne abin da zamu mayar da hankali kai. Ba zamu iya sadaukar da su kan dalilan siyasa ba. Bukatun siyasa ba zai sha gaban aiwatar da aikin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Zabo Tinubu ya ba mutane da yawa mamaki, Garba Shehu ya yi magana mai daukar hankali

"Muna da gadoji da tituna da za mu gina ba wai don kasuwanci da tafiye-tafiye kadai ba amma don sada mutane masu mabanbantan addini, jam'iyya da ra'ayoyi don tattaunawa da cimma matsaya guda.
"Muna da iyalai da za mu ciyar ba wai kawar da yunwa kadai ba amma tare da wayar da kai, sauka nauyin da kasa ya dora masa da tausayi."

Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya su rungumi gwamnatinsa

Hakazalika, zababben shugaban kasar ya yi kira ga yan kasa su yi aiki tare da gwamnatinsa, su kuma yi aiki tare da wadanda ba su goyi bayansa ba yayin zabe.

Ya ce aikin gina kasa nauyi ne da ya rataya kan dukkan yan kasa baki daya.

Uba Sani: Kawancen da PDP ta kulla da sauran jam'iyyu ba ya tayar min da hankali

A wani rahoton, Sanata Uba Sani, dan takarar gwamnan APC a Kaduna ya ce hadin gwiwar da jam'iyyar PDP, ta yi da wasu jam'iyyun siyasa a jihar ba ya tayar masa da hankali ko kadan.

Kara karanta wannan

Canjin kudi, Kanu, ASUU da Abubuwa 5 da Tinubu Zai Ci Karo da Su da Ya Shiga Aso Rock

Ya furta hakan ne yayin wata tattauna da aka yi a gidan talabijin na Arise gabanin zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel