Jam'iyyu 30 Sun Mara Wa Jam'iyyar Kwankwaso Baya A Zaben Gwamnan Ogun
- Jam'iyyu masu rijista da marasa rijista a Jihar Ogun sun dunkule tare marawa dan takarar gwamnan Jihar a jam'iyyar NNPP baya
- Jam'iyyun sun ce bayan dogon nazari da su ka yi don cigaban jihar da ceto ta daga halin da ta ke ciki, sun yanke shawarar marawa Oguntoyinbo na NNPP baya
- Oguntoyinbo, ya godewa jam'iyyun tare da alkawarin ba zai bawa mara dan kunya ba idan aka kai ga nasara a zaben da za a gudanar ranar Asabar
Ogun - Kasa da awanni 48 kafin zaben gwamnoni, jam'iyyu goma da kuma karin guda ashirin marasa rijista a Jihar Ogun sun janye takara-sun kafa kugiya, sun kuma amince tare da marawa dan takarar gwamnan Jihar na jam'iyyar NNPP, Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo.
Jam'iyyun sun hada da African Democratic Congress (ADC), Labour Party (LP), African Action Congress (AAC), Action Alliance (AA), Allied Peoples Movement (APM) da Social Democratic Party (SDP).
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sannan akwai jam'iyyar National Rescue Movement (NRM), All People’s Party (APP), Action Democratic Party (ADP), Boot Party (BP), Atiku Support Group da wasu.
An bayyana hadakar ranar Alhamis a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, rahoton Tribune.
Jam'iyyun sun bayyana dalilin janye wa dan takarar gwamnan na NNPP a Ogun
Da su ke jawabi a madadin jam'iyyun da suka hade kan dalilin marawa dan takarar NNPP baya, Olowo John Bolaji, Sokeye Oluwalogbo, Sonde Rasaq, Amusa Sefiu, Bolaji Sunday da sauransu sun cewa sun yanke shawarar a ceto Jihar Ogun, suna masu cewar shekara hudun Gwamna Dapo Abiodun ya mayar da jihar baya ta fannin cigaban da sauran gwamnoni suka kawa da kuma mayar da Jihar Ogun zamanin baya.
Ya ce:
''Jihar ta tsaya cak tsahon shekaru a hannun shugabannin da su ka shude a jihar nan kuma dole mu yi amfani da wannan damar da dimukradiyya ta ba mu.
2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Balle Daga Hadakarta Da Jam'iyyar Peter Obi, Ta Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce
''Mun yarda domin gyara wannan kuskuren, dole mu hada karfi da karfe da jam'iyyar da zata iya kawar da wannan gwamnati da ya tabbata bata da hanyoyin kawo cigaba.
''Shi yasa, bayan tattaunawa da dama tare da masu ruwa da tsaki daga wajen jam'iyyarmu, muka yanke cewa Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo na jam'iyyar NNPP."
Ya cigaba da cewa:
''Matakin ba shi da alaka da komai face cigaban jiharmu. Yana da tarihi. Shi ba irin mutanen da suke alkawari su saba bane. Mutum ne mai magana daya. Da wannan na ke kira da mu fito kwan mu da kwarkwata mu kada ma sa kuri'a."
''A watanni 46 da suka wuce, gwamnati ta zama wani abu daban a Jihar Ogun. Don ceto mu, mu na kira ga kowa da ya isa zabe cewa ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023, za mu zartar da hukunci da zai bayyana matsayar jiharmu nan da shekaru hudu masu zuwa.
''Ba shawara ce da aka yanke saboda kabilanci, jam'iyya ko bangarancin addini. Ba shawara ce ta son mukami ko soyayya ba. Wannan ce damarku ta hanyar zabar dan takarar da ya cancanta kuma ya ke da kwarewa, juriya, nagarta da kuma kyakkyawan tarihi da ke nuni da yadda za a samu kyakkyawan shugabanci a jiharmu.''
Martanin Oguntoyinbo
Da ya ke jawabi bayan an dawo tafiyarsa, dan takarar gwamnan na jam'iyyar NNPP, Oguntoyinbo ya gode wa yan jam'iyyar da su ka dawo tafiyarsa saboda yarda da cancantarsa, juriyarsa da kuma gamsuwa zai ciyar da Jihar Ogun gaba.
Ya yi alkawarin mayar da Jihar Ogun abar kwatance tare da tabbatarwa al'umma ba zai ba su kunya ba.
Kwankwaso ne zai gaji Buhari - Bashir El-Rufai'i
A bangare guda, kun ji cewa daya cikin yayan gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Bashir, ya ce Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasan jam'iyyar NNPP a zaben 2023 ne zai zama 'magajin Shugaba Muhammadu Buhari.'
Bashir ya ce masu yiwa Kwankwaso dariya zasu sha mamaki a nan gaba.
Asali: Legit.ng