Zaben Shugaban Kasa: IPOB Na Yi Wa Peter Obi Aiki, Jigon APC Ya Bayyana Dalilai
- Wani jigon APC, Biodun Ajiboye, ya zargi Peter Obi, dan takarar jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa da amfani da IPOB yayin zabe
- Ajiboye ya na ganin cewa kungiyar masu fafutukar sun goyi bayan Peter Obi saboda bai taba nuna rashin goyon bayansa ga ayyukan kungiyar ba
- A cewar Ajiboye, Obi yayi amfani da addini da al'ada a matsayin abin da ya bashi nasara a Lagos
Biodun Ajiboye, wani jigon jam'iyyar APC a Jihar Lagos, ya zargi kungiyar masu fafutukar kafa Biafra IPOB da marawa Peter Obi, na jam'iyyar Labour baya a zaben shugaban kasa da aka gudanar a baya bayan nan.
Jigon APC ya yi wannan ikirarin lokacin da ya ke mayar da martani lokacin da ya ke amsa tambaya akan dalilin da ya jam'iyyar ta sha kayi a hannun jam'iyyar LP a Jihar Lagos, duk da kasancewar jihar na hannun jam'iyyar kuma daga nan dan takarar shugaban kasar jam'iyyar ya fito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jam'iyyar APC ta Tinubu ta shan kayi a hannun Peter Obi a Lagos lokacin zaben shugaban kasa
Da ya ke bayyana dalilin da ya janyo Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, ya sha kayi a hannun Peter Obi, Ajiboye ya jaddada cewa matasa da yawa suna cikin fushin abin da ya faru lokacin zanga-zangar EndSARS a Lagos.
Ya kuma bayyana cewa ciki hadda tikitin Muslim-Muslim na jam'iyyar APC, ya kuma kara da cewa Peter Obi ya yi amfani da addini ta hanyar zuwa Cocina da fada mu su cewa ''su ceto kasarsu'' kai ka ce Najeriya ta addini daya ce.
Ajiboye ya kuma zargi tsohon gwamnan na jihar Anambra da amfani da addini, yana mai cewa duk kabilar Igbo na Lagos da kuma yankin kudu maso gabas sun kada kuri'un su ga Peter Obi kuma abin takaici ne yan kungiyar fafutukar Biafra, IPOB, sun masa aiki.
Da Zafi-Zafi: Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili
Ya bayyana cewa tun lokacin da IPOB suka ayyana dokar zaman gidan dole tana nan daram, Peter Obi, bai taba sukar ayyukan IPOB ba, duk da kashe yan sanda da sauran jami'an tsaro.
An kuma zargi IPOB na kona ofisoshin yan sanda da na hukumar zabe a yankin kudu maso gabas da kuma ikirarin cewa ba za a gudanar da zabe a yankin ba, amma, Obi ya samu gagarumar nasara a yankin.
Kalli bidiyo a kasa:
Bashir El-Rufai: Kwankwaso ne zai gaji Buhari
Bashir El-Rufai, daya cikin yayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023 ne zai zama 'magajin Shugaba Muhammadu Buhari.'
Bashir ya ce masu yi wa Kwankwaso dariya za su sha mamaki a nan gaba.
Asali: Legit.ng