Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

  • Kashim Shettima ya wakilci Asiwaju Bola Tinubu, ya zauna da zababbun ‘Yan majalisar tarayya
  • Bola Tinubu ya nuna duk wanda ‘Yan majalisa suke so ya zama Shugabansu a 2023, yana tare da shi
  • Wasu ‘yan majalisar sun tabbatar da zaben Gwamna da na ‘Yan Majalisa ne a gaban Bola Tinubu

Abuja - A ranar Litinin, Asiwaju Bola Tinubu ya shaidawa wadanda za su zama ‘yan majalisa cewa bai da wani ‘dan takara a mukaman da za a raba.

Jaridar Sun ta ce zababben shugaban kasar ya bayyana haka ne a jawabinsa, da yake bai samu halartar zaman ba, Sanata Kashim Shettima ya wakilce shi.

Masu neman kujeru a majalisar wakilan tarayya da na dattawa su na ta kokarin kamun kafa, shugaban Najeriyan mai jiran gado bai tare da kowa.

Kara karanta wannan

Tinubu: "Ban San Batun Kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Aso Rock ba" - Gbajabiamila

Ganin a 2015, wadanda jam’iyya ba ta so sun karbe shugabancin majalisa, babu mamaki shiyasa wannan karo APC take kokarin yi wa tufkar hanci.

Ba ayi kason mukamai ba

Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya jagoranci taron. An yi tunani a zaman na jiya, za ayi kason mukamai amma ba hakan ya faru ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton da aka fitar ya ce Festus Adefiranye wanda zai wakilci mazabar Ileoluji/Okeigbo/Odigbo ya ce Kashim Shettima ya karanto jawabin Bola Tinubu.

Asiwaju
Asiwaju Tinubu da Shettima a kamfe Hoto: officialasiwajubat
Asali: Twitter

A madadin Tinubu, zababben mataimakin shugaban na Najeriya ya yi kira ga wadanda aka zaba suyi aiki tare, su zabi shugabannin da suka yarda da su.

‘Dan siyasar ya ce za a gabatarwa jam’iyya da duk wanda ‘yan majalisar suka zaba, dalilin haka shi ne a tabbatar da adalci da gaskiya da tsarin karba-karba.

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

Zaben Jihohi ya hana Tinubu zuwa Abuja

‘Dan majalisar Ilaje/Ese Odo na jihar Ondo, Donald Ojogo ya ce Bola Tinubu bai samu zuwa taron ba ne domin su na tsara yadda za a tunkari zaben makon nan.

Ganin yadda zaben shugaban kasa ya kasance, Tinubu zai so jam’iyyarsa ta APC ta zarce a jihar Legas tare da samun nasarar ‘yan takaransu a majalisar jiha.

Da ya zanta da ‘yan jarida, This Day ta rahoto Hon. Abdulmalik Bungudu ya ce batun wadanda za su zama shugabanni majalisa bai gaban Tinubu a yanzu haka.

Majalisa sai Iyan Zazzau

Gwamna El-Rufai ya fito da ‘Dan takaran shugaban najalisa, an ji labari zai gana da Bola Tinubu domin neman alfarmar kujerar shugabancin majalisar wakilai.

Nasir Ahmad El-Rufai zai hadu da Bola Tinubu a kan batun goyon bayan Hon. Abbas Tajudeen mai wakiltar mazabar Zariya a Kaduna domin ya rike Majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng