Katsina: ‘Dan Takaranmu a Zaben 2023 Bai Cancanta Ba – Shugaban Jam’iyyar NNPP
- Shugaban Jam’iyyar NNPP da aka dakatar a Katsina ya yi wa majalisar gudanarwa raddi
- Sani Liti ya yi karin haske a kan dalilinsu na marawa Dr. Umar Dikko Radda baya a zaben Gwamna
- Alhaji Liti ya ce ba su sauya-sheka ba, a zaben Gwamnan jiha ne kurum suke tare da Jam’iyyar APC
Katsina - Shugaban Jam’iyyar NNPP na reshen jihar Katsina, Sani Liti ya soki ‘dan takaransu na Gwamnan jihar Katsina a zaben nan na 2023.
Alhaji Sani Liti ya ce Injiniya Nura Khalil da aka tsaida, bai cancanci ya zama Gwamna a jihar ba. Za a samu wannan labari a The Nation.
Shugaban na NNPP ya bayyana haka ne a yayin da ya kira taron manema labarai, yana mai maida martani kan korarsu da aka yi daga jam’iyya.
Alhaji Nasiru Usman-Kankia ya fitar da jawabi da yawun jam’iyya, ya ce an kori Sani Liti, Dr. Rabe-Darma da wasu shugabannin NNPP na jihar.
Dikko Radda ya fi Nura Khalil?
A jawabin da ya yi, Sani Liti ya ce dole ta sa shugabannin jam’iyyar adawa ta NNPP suka yi wa ‘dan takaran APC mubaya’a domin ya fi cancanta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ra’ayin ‘dan siyasar da wasu jagororin jam’iyyarsu a Katsina, Dr. Umar Dikko Radda zai fi yin kokari a matsayin Gwamna idan har ya samu dama.
Bayan duba halin da ake ciki a jam’iyya da shirin zabe (na Gwamnan Katsina), mun yarda mu goyi bayan duk ‘yan takaran majalisar dokokin jiha.
Kuma za mu yi kokarin da za mu iya wajin ganin sun samu nasara a zaben 18 ga Maris. Sannan mu na tare da jagoranmu, Dr. Rabiu Kwankwaso.
- Sani Liti
Taron da aka yi ya saba doka
A rahoton Vanguard, Liti ya ce mai magana da yawun bakin jam’iyyarsu ya kira taron shugabanin jiha ne ba da umarnin shugaban kwamitin ba.
Shugaban na NNPP ya ce taron da ya samu halartar wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar ya saba sashe na tara na dokar NNPP, don haka za suyi bincike.
Farfesa Sanusi Jari zai binciki wadanda ake zargi da saba doka, amma kafin nan an dakatar da Kakaki, mataimakinsa, ma’aji da sakataren walwala.
An daure 'Yan PDP
Alkali ya gamsu da hujjojin EFCC, an ji labari an samu Sale Hussaini Gamawa da Aminu Umar Gadiya da laifin karbar N140m a kakar zaben 2015.
Kotu ta yi masu rangwame ganin su na da iyali, amma an yi masu hukuncin da zai zama darasi ga ‘yan baya, za su shekara biyu a gidan gyaran hali.
Asali: Legit.ng