"Zan Tona Asirin Tsofaffin Gwamnonin Da Suka Sace Dukiyar Jihar Kaduna", El-Rufai

"Zan Tona Asirin Tsofaffin Gwamnonin Da Suka Sace Dukiyar Jihar Kaduna", El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa yana dab da tona asirin wasu tsofaffin gwamnonin jihar
  • A cewar gwamnan idan tsofaffin gwamnonin basu dai na yi masa katsalandan ba, to zai gayawa duniya irin satar da suka tafka a jihar
  • El-Rufai ya bayyana tsofaffin gwamnoni a matsayin ɓarayi waɗanda suka sanyawa dukiyar jihar wasoso

Jihar Kaduna- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yayi barazanar tona asirin tsofaffin gwamnonin jihar waɗanda suka wawushe dukiyar jihar. 

Ya yi musu gargaɗin cewa idan har suka cigaba da buɗe baki suna gaya masa magana, to zai zama baya da wani zaɓi face ya gayawa duniya yadda suka yi awon gaba da dukiyar jihar. Rahoton Vanguard

El-Rufai
"Zan Tona Asirin Tsofaffin Gwamnonin Da Suka Sace Dukiyar Jihar Kaduna", El-Rufai Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Yayi zargin cewa kuɗaɗen da suka wawushe sun kai su ƙasahen Turai da Dubai, da wasu birane a ƙasar Amurka inda suka mallaki kadarori.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan CBN Ya Umurci Bankuna Su Fara Fitar da Tsaffin Kudi, Gov Soludo

A cewar sa, ɗaya daga cikin tsofaffin gwamnonin yana da hannu dumu-dumu a ɓacewar N500m kuɗin kwangilar sake gina titin WAFF road, domin babu abinda akayi a hanyar har sai da ya zama gwamna ya mayar da ita mai hannu biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sun kwashe kuɗin, mutumin da suka ba kwangilar titin WAFF road ya rasu." A cewar gwamnan

Sai dai, gwamnan ya nuna yatsa kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, wanda ya fara ginin asibitin ƙwararru mai gadaje 300 a Kaduna amma ya kasa kammala aikin saboda sulalewar da yayi zuwa Abuja babu shiri.

"Dukkanin su ɓarayi ne, na san yadda suke a baya sannan kalli matsayin da suke da shi a yanzu. Ɗaya daga cikin su har wani katafaren gida ya gina a Jabi cikin Kaduna."
"Ina ƙalubalantar duk wani wanda ya san gwamnatin mu na karɓar kamashon kaso 10 daga wajen ƴan kwangila. Amma wadannan mutanen suna karɓar kamashon kaso 10."

Kara karanta wannan

"Na rantse da Allah ban taba ɗaukar sisin Jihar Kaduna ba, wanda ya Ƙaryata Yazo Mu Dafa Kur'ani" - El-Rufai

Ba Tinubu Bane Zabin Allah’: Peter Obi Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Kalaman Aisha Buhari

A wani labarin na daban kuma, Peter Obi, ya tono silar nasarar Tinubu ta zama.zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya.

Ɗan taƙarar na jam'iyyar Labour Party, yana daga cikin ƴan takarar da suka yi rashin nasara a hannun Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel