Muhimman Abubuwan Sani Game Da Manyan Ƴan Takarar Gwamnan Bauchi 2

Muhimman Abubuwan Sani Game Da Manyan Ƴan Takarar Gwamnan Bauchi 2

A ranar Asabar 18 ga watan Maris mai zuwa al'ummar jihar Bauchi, zasu yi dafifi a rumfunan zaɓe domin zaɓar gwamnan da zai mulki jihar su, a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokoki na jiha da za ayi a faɗin Najeriya.

Ƴan takara biyu ne dai ke kan gaba a wannan zaɓen na gwamnan jihar Bauchi. Legit.ng Hausa tayi duba akan waɗannan ƴan takara guda biyu domin haska muku wasu abubuwa da suka shafi rayuwar su.

Gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP, Bala Mohammed, da ɗan takarar jam'iyyar APC, Sadique Abubakar, sune ake yiwa hasashen ɗaya daga cikin su zai lashe zaɓen.

Gwamna Bala Muhammad na jam'iyyar PDP

1. Haihuwa

An haifi Bala Muhammad a ranar 5 ga watan Octoban 1958, a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi. Rahoton BBC Hausa

Kara karanta wannan

An Shiga Rudani a Kano Kan Sauya Kwamishinoni 'Yan Sanda Da IGP Yayi a Jihar Ana Dab Da Zabe

Bauchi
Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad Hoto: Premium Times
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Karatu

Yayi karatun firamaren sa daga 1965 zuwa 1971 a wata makaranta a ƙauyen Duguri. Yayi karatun sakandire daga shekarar 1972 zuwa 1976.

Ya halarci kwalejin kimiyya da zane-zane ta yankin Arewa maso Gabas daga shekarar 1977 zuwa 1979.

Yayi karatun digirin sa na farko a jami'ar Maiduguri a fannin Ingilishi daga shekarar 1979 zuwa 1982.

3. Aiki

Bala Mohammed ɗan jarida wanda yayi aiki da jaridu da dama. Yayi aiki da jaridar The Mirage daga shekarar 1982 zuwa 1983.

Yayi aiki da jaridar The Democrat daga shekarar 1983 zuwa 1984.

Yayi aiki da ma'aikatar cikin gida ta Najeriya daga shekarar 1984 zuwa 1994. Ya zama babban jami'in shigo da kayayyaki a ma'aikatar albarkatun ƙasa daga shekarar 1995 zuwa 1997.

Bala Mohammed ya taɓa zama mataimakin darakta a ma'aikatar wuta ta Najeriya daga shekarar 1997 zuwa 1999. Ya zama darektan gudanarwa a hukumar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya a shekarar 2003.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

4. Siyasa

Ya zama ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Bauchi ta Kudu daga shekarar 2007 zuwa 2010 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ANPP.

Yayi ministan birnin tarayya Abuja daga shekarar 2012 zuwa 2015. Ya zama gwamnan jihar Bauchi a shekarar 2019 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

5. Sarauta

Gwamna Bala Muhammad yana riƙe da sarautun gargajiya guda uku waɗanda suka haɗa da Ƙauran Bauchi, Dangaladiman Duguri da Agunachebe Umueje.

Abubakar Sadique na jam'iyyar APC

Akwai muhimman abubuwa game da rayuwar Abubakar Sadique dan takarar gwamnan Bauchi na jam'iyyar APC. Mun tsinto muku kaɗan daga ciki kamar haka;

1. An haifi Sadique Baba Abubakar a ranar 8 ga watan Afrilun 1960 a ƙaramar hukumar Azare ta jihar Bauchi. Rahoton Military History

Abubakar
Sadique Baba Abubakar, Ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na APC Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

2. Yayi karatun firamare a makarantar St Paul a Bauchi da karatun sakandire a makarantar sakandiren gwamnati ta Bauchi.

3. Yana da kwalin difloma a fannin 'Public Administration da kwalin digiri a fannin kimiyyar siyasa. Yana da kwalin digirin digir a fannin 'Strategic Studies' daga jami'ar Ibadan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

3. Ya fara aiki da rundunar sojin sama ta Najeriya a shekarar 1979. Yayi ta samun ƙarin girma inda har ya kai ga matsayin babban hafsan rundunar a shekarar 2015.

4. Ya riƙe muƙamai da yawa a rundunar inda ya samu lambobin yabo masu tarin yawa a shekarun da ya kwashe yana aiki da su.

5. Yayi ritaya a ranar 26 ga watan Janairun 2021.

6. A yanzu yana takarar zama gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng