Fadar Shugaban Kasa ta fadi abin da zai hana a damka shugabanci a hannun Bola Tinubu
- Fadar shugaban kasa ta fadawa Jam’iyyun PDP da LP cewa Bola Tinubu zai karbi mulkin kasa
- Malam Garba Shehu ya ce babu abin da zai hana Tinubu ya shiga Aso Villa sai hukuncin kotu
- Zababben Shugaban Najeriyan da bakinsa ya taba cewa ba za a soke zaben 2023 kamar a 1993 ba
Abuja - Fadar shugaban kasa ta jaddada cewa nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa tana nan, sai dai idan kotu ta ce ba haka ba.
Vanguard ta rahoto Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai da hulda da jama’a, Malam Garba Shehu yana mai wannan maganar.
Garba Shehu ya bayyana haka a rubutun da ya yi domin nuna nasarorin da Muhammadu Buhari ya samu da ya ziyarci birnin Doha a Qatar.
Mai magana da yawun na shugaba Muhammadu Buhari ya ce masu sukar INEC a game da zaben bana, su na fadan abin da suka ga dama ne.
Buhari ya yi banza da masu surutai
Hadimin ya ce shugaban kasa ba zai yi abin da zai iya taba martabar zaben da aka gudanar ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An rahoto Garba Shehu yana cewa Mai gidansa ya yi kunnen uwar-shegu ga masu wadannan surutai a Najeriya ne ta hanyar fita zuwa kasar waje.
A rubutun da ya yi, Mai magana da yawun shugaban ya ce mai ja da sakamakon zaben, ya garzaya kotun korafin zabe domin ya shigar da kara.
Punch ta ce fadar shugaban kasa ta na zargin wadanda suke tir da zaben shugaban kasar da aka yi a Fubrairun 2023 su da wata muguwar manufa.
Maganar da Garba Shehu ya yi
"Nasarar Bola Tinubu a zabe ta na nan. Idan ka fusata, kuma dama ka na da hakki, sai ka tafi kotu.
Burin hakan shi ne a jefa mutane a cikin razani, a jawo firgici a cikin al’umma, a bata sunan gwamnati.
Masu wannan tunani su na ganin za a iya dawo da rikicin Yunin 1993, mafi muni bayan yakin basasa.
Wadanda ke wannan sun manta da abin da zababben shugaban kasar ya fada a fadar Gbong-Gwon Jos.
Da ya je birnin domin bude kamfe, Tinubu ya ce ba za a soke zabe ba ko wanene zai zama shugaban kasa."
- Garba Shehu
Yadda Tinubu ya ci zabe - Sanata Iyiola Omisore
An samu labari Sakataren APC, Iyiola Omisore ya ce hadin-kan ‘Yan APC ya jawo Bola Tinubu ya iya dankara Atiku Abubakar da Peter Obi da kasa.
Sanata Iyiola Omisore ya karyata ‘Yan takaran PDP da LP, ya ce ba ayi magudin zabe ba ganin yadda APC ta rasa Katsina, Nasarawa, Filato da Legas.
Asali: Legit.ng